Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi?3
Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu: Amfani da karfi bai […]
Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Amfani da karfi bai dace ba – Dokta Chindo
Dokta Chindo Shu’aibu: “Wannan batu yana bukatar a koma kan gaskiya, a fuskanci lamarin bisa adalci, a saki wadanda aka kama ba da laifi ba. Bayan haka wadanda aka kashe masu ’yan uwa bisa kuskure ko ganganci da nuna fin karfi, a biya su diyya, a kuma ba su hakuri. Daga nan sai a fara neman mafita ta gaskiya. Amma ba zai yiwu a maida wasu marayun dole wasu kuma ana tsare da su ba tare da sun aikata wani laifi ba kuma ba a kai su kotu ba, sai gallazawa sannan a ce an kafa wasu kwamitoci na sasantawa ko kuma an kara tsawaita dokar ta baci don ganin karshen wannan lamari ba.