Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi?4
Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu: Sulhu zai samar […]
Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Sulhu zai samar da mafita – Ruslanu Khalil
Ruslanu Khalil: “Ra’ayina shi ne, amfani da karfi kan ’yan Boko Haram ba zai yi maganin abin ba, domin ko yaki ya barke, idan abin ya ki cinyewa, dawowa ake yi a yi sulhu, sai a samar da mafita da matsaya guda daya. An sami gwamnati tana iya bakin abin da za ta iya yi amma wannan ba shi ne mafita ba. Mafita ita ce a nemi sulhu da su amma ba amfani da karfi ba. Wannan ba zai magance matsalar ba.”