Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi?5
Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu: karfi ba shi […]
Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
karfi ba shi ne magani ba – Aminu Abdullahi
Aminu Abdullahi: “A ra’ayina, babu yadda za a yi sanya karfi ya yi maganin kungiyar Boko Haram, sai dai a yi sulhu da su. Har yanzu wadanda ake sanyawa a tsakanin kungiyar da gwamnati ba a dace ba ne kuma ai ka ji ana cewa duk abin da zaman lafiya bai kawo shi ba, to tsiya ba za ta yi maganisa ba. Don haka sanya karfi ba zai magance wannan matsalar ba, don ba a ma san ko su wane ne ba. A ci gaba dai da neman sulhu da su, za a dace wata rana.”