Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi?6
Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu: Sulhu kadai zai […]
Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Sulhu kadai zai magance matsalar – Iliya Yakubu
Iliya Yakubu: “Ina ganin bai kamata gwamanti ta ci gaba da yin amfani da karfi wajen maganin wannan matsala ba, domin wanda ta yi a baya ma bai warware matsalar ba. Batun sulhun nan dai shi ya kamata gwamnati ta tsaya a kansa. ’Yan kwamitin su nemo ’ya’yan kungiyar su zauna da su a ci gaba da yin sulhu har Allah Ya kawo karshen lamarin. Amma yin amfani da karfi da gwamnati ke yi a kansu shi ne yake tunzura su suke kara kai hare-hare a kullum.”