Ko za a samar wa matasa makoma tagari a Zamfara?
Ranar 1 ga watan 11 ce ranar matasa da qungiyar hada kan Afirka ta ware, domin tunawa da manyan gobenta, tare da qoqarin nema wa matasanta mafita, a kan wasu matsaloli da matasan suke fuskanta, domin magance su. Bisa la’akari da cewa matasa su ne qashin bayan cigaban kowa ce al’umma, inda har masu iya […]
Ranar 1 ga watan 11 ce ranar matasa da qungiyar hada kan Afirka ta ware, domin tunawa da manyan gobenta, tare da qoqarin nema wa matasanta mafita, a kan wasu matsaloli da matasan suke fuskanta, domin magance su. Bisa la’akari da cewa matasa su ne qashin bayan cigaban kowa ce al’umma, inda har masu iya magana ke cewa; “duk al’ummar da matasanta suka zama nagari, to tabbas al’ummar za ta ci gaba.”
Ganin hakan ne kai tsaye sai na hango jihar da nake rayuwa a cikin, kasancewar nan ne, mai duka ya halicce ni, wato Jihar Zamfara. Domin farawa da gida shin wane hali ‘yan uwana matasan Jihar Zamfara muke ciki?
Shin gwamnatinmu na kula da mu?
Shin tana ba mu ilimi ingantacce kuma wadacce?
Shin tana yin iya yinta domin nema wa matasa makoma tagari?
Shin ta kula da yadda muke neman abin zaman gari?
Shin dattawanmu da ‘yan siyasarmu sun kula da mu?
Wadannan su ne jerin tambayoyin da na yi wa kaina, tare da yin nutso a kogin tunani, domin gano amsarsu, tun daga lokacin da aka danqa mulkin jihar ta mu a hannun farar hulla a 1999 zuwa yau . Abin da na tabbatar shi ne gaskiya gwamnatocin da suka gabata, musamman gwamnatin farar hula ta farko ta taka muhimmiyar rawa wajen sama wa matasa makoma tagari, musamman ta bangaren neman ilimi, qirqiro da hanyoyin dogaro da kai ga matasa da ma musakai. Hakan ta taka muhimmiyar rawa wajen bai wa qananan ‘yan kasuwa bashi tare da yafe musu in sun turza da biya.
Amma sai kash! Duk da shi gwamna mai ci a yanzu yana cewa wai fa yana koyi ne da maszahabar gwamnan farar hular Zamfara na farko. Amma kwata-kwata ya watsar da koyarwar da mazahabar baki daya, musamman wajen taimaka wa matasa ta kowane fanni. Idan muka dauki bangaren ilimin matasa, rashin daukarsu aiki. Ba a qarfafa su ba, ni na manta lokacin da wani makaho ya isko ni yana cewa “Don Allah Abdulmalik ku taimaka ku shaida wa Gwamna Shehi cewa, ‘tun da gwamnatinsa ta hau mulki kwata-kwata bai waiwayo mu ba, duk da bayan ya yi iqirarin cewa mu musakai ne muka saya masa tikitin tsayawa takara a zangonsa na biyu. Har ya yi mana alqawarin zai yi hukuma ta musamman ta musakai, domin taimaka wa musakai tare da ba su alawus, domin ya daina bara. Amma har yanzu bai waiwayo mu ba har ‘yar cibiyar da muke aiki, ciki yau shekaru biyar ke nan, kwata-kwata ba kaya. Don Allah ku taimaka muna neman agaji”
Wannan ke nan duk wani mazauni Jihar Zamfara ya san an yi shekaru da rufe babbar cibiyar koyar da matasa sana’o’in hannu da ke Gusau, inda dubban matasa ne maza da mata suke amfana da ita, ta hanyar koyon sana’o’in da za su dogara da su. Har yanzu ba mu ji an fada mana dalilin rufe cibiyar ba, duk da alfanun da take da shi ga matasan Jihar Zamfara.
Yau sama da shekaru shida da rabi ke nan da gwamnatin nan ta hau karagar mulkin jihar, amma har yau ba ta dauki matashi daya aiki ba, sai dai korar wadanda ta isko da ta yi bayan ta fake da cewa na bogi ne.
Maganar bai wa matashin Jihar Zamfara qwarin guiwar ya tashi ya nemi ilimi kuwa har mu matasa mun manta da cewa gwamnatocin jihohin na taimaka wa matasa ta hanyar neman ilimi, babu tallafin karatu har ‘yar Waec da Neco din da daga shekara sai shekara gwamnati ke biya, an wayi gari sai dalibai sun fitar da rai daga fitowarta, sannan gwamnati ke biya har ta zo gunsu. Wanda hakan kan haifar da tabarbarewar ilimi tare da tilasta wa matasan barin jihar domin neman abin sawa a bakin salati a sauran jahohin qasar nan. Wasu kuwa tuni sun zama baqin haure masu hakar ma’adanai ta barauniyar hanya, a qasashe makwabtanmu.
Don haka ya kamata Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi karatun ta natsu, domin waiwayo matasanta. don wallahi muddin aka tafi a haka duk wani Bazamfare Sai ya koka.
Don gudun kada a wayi gari al’ummar jihar jahilai za su fi rinjaye. Kuma duk inda jahilci ya yi rinjaye dole matsaloli su yi katutu.
Dattawanmu na Jihar Zamfara da sauran ‘yan siyasarmu ya kamata ku farka daga dogon sumar da kuka yi, ku fada wa gwamnati gaskiya in ta dauka to, in kuma ba ta dauka ba, kun fita.
Domin wallahi shirunku illa ce babba ga jihar mu.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami’in Hulda Da Jama’a Na Kungiyar Matasan Zamfara Ta Tsakkiya) 08069807496 <[email protected]>