Ko za ka iya daina musafaha sabo 3da tsoron cutar Ebola? 3
A halin da ake ciki dai labarin bazuwar cutar Ebola ya zama ruwan dare, lungu da sako duk ya shiga, wanda haka ya haddasa tsoro da zullumi a zukatan al’umma. Kasancewar daya daga hanyoyin daukar cutar shi ne hada jiki da mai cutar, wasu suna ganin yin musafaha ko gaisuwar hannu-da-hannu ma hadari ne a […]
A halin da ake ciki dai labarin bazuwar cutar Ebola ya zama ruwan dare, lungu da sako duk ya shiga, wanda haka ya haddasa tsoro da zullumi a zukatan al’umma. Kasancewar daya daga hanyoyin daukar cutar shi ne hada jiki da mai cutar, wasu suna ganin yin musafaha ko gaisuwar hannu-da-hannu ma hadari ne a wannan zamanin. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko za ka iya daukar matakin daina irin wannan gaisuwar saboda tsoron wannan cuta ta Ebola? Ga ra’ayoyin wasu daga al’umma, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Ba za ta hana ni gaisuwa ba – Aliyu dahiru
Aliyu dahiru Osun: “Har yanzu dai bayanin cutar Ebola na matsayin jita-jita ne tukunna saboda babu hakikanin tabbatuwar ta. Kuma ko da ta zama gaskiya, tsoron kamuwa da ita ba zai hana ni musafaha da jama’a ba saboda sunnah ce ta manzon Allah (SAW). Kuma a yadda nake ji, mai fama da ita ba zai iya fitowa ba saboda matsalarta bare ma har a yi musafaha da shi.”