Ko za ka iya daina musafaha saboda tsoron cutar Ebola?
A halin da ake ciki dai labarin bazuwar cutar Ebola ya zama ruwan dare, lungu da sako duk ya shiga, wanda haka ya haddasa tsoro da zullumi a zukatan al’umma. Kasancewar daya daga hanyoyin daukar cutar shi ne hada jiki da mai cutar, wasu suna ganin yin musafaha ko gaisuwar hannu-da-hannu ma hadari ne a […]
A halin da ake ciki dai labarin bazuwar cutar Ebola ya zama ruwan dare, lungu da sako duk ya shiga, wanda haka ya haddasa tsoro da zullumi a zukatan al’umma. Kasancewar daya daga hanyoyin daukar cutar shi ne hada jiki da mai cutar, wasu suna ganin yin musafaha ko gaisuwar hannu-da-hannu ma hadari ne a wannan zamanin. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko za ka iya daukar matakin daina irin wannan gaisuwar saboda tsoron wannan cuta ta Ebola? Ga ra’ayoyin wasu daga al’umma, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Bai dace a daina ba – Ghali Sulaiman
Bashir Rabi’u Jiwa: “A gaskiya ba za ta hana ni musafaha da jama’a ba kuma ni ban ma yarda akwai cutar ba. Ko da akwai ta kuwa, abu guda da na sani shi ne, idan mutuwata ta zo ba makawa mutuwa zan yi ko da cutar ko babu ita. Sannan idan da sauran numfashina kuma, ba Ebola ba koma mene ne ba zan mutu ba.”