Ko za ka iya daina musafaha saboda tsoron cutar Ebola? 2
A halin da ake ciki dai labarin bazuwar cutar Ebola ya zama ruwan dare, lungu da sako duk ya shiga, wanda haka ya haddasa tsoro da zullumi a zukatan al’umma. Kasancewar daya daga hanyoyin daukar cutar shi ne hada jiki da mai cutar, wasu suna ganin yin musafaha ko gaisuwar hannu-da-hannu ma hadari ne a […]
A halin da ake ciki dai labarin bazuwar cutar Ebola ya zama ruwan dare, lungu da sako duk ya shiga, wanda haka ya haddasa tsoro da zullumi a zukatan al’umma. Kasancewar daya daga hanyoyin daukar cutar shi ne hada jiki da mai cutar, wasu suna ganin yin musafaha ko gaisuwar hannu-da-hannu ma hadari ne a wannan zamanin. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko za ka iya daukar matakin daina irin wannan gaisuwar saboda tsoron wannan cuta ta Ebola? Ga ra’ayoyin wasu daga al’umma, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Ba zan daina musafaha ba – Usman Lapai
Usman ibn Abdullahi Lapai: “Maganar musafaha ba ta da wata alaka da yada cutar Ebola saboda haka a matsayina na Musulmi ba zan daina musafaha da mutane ba saboda addinina na Musulunci ne ya umurce ni da yin musafaha. Sai dai zan yi kokari in rika lura da kuma tabbatar da cewa idan na yi musafaha da mutane zan rika wanke hannuna kafin cin abinci kamar yadda masana kiwon lafiya suka umurta da yi, domin kauce wa cutar.”