Ko za ka iya daina musafaha saboda tsoron cutar Ebola? 3
A halin da ake ciki dai labarin bazuwar cutar Ebola ya zama ruwan dare, lungu da sako duk ya shiga, wanda haka ya haddasa tsoro da zullumi a zukatan al’umma. Kasancewar daya daga hanyoyin daukar cutar shi ne hada jiki da mai cutar, wasu suna ganin yin musafaha ko gaisuwar hannu-da-hannu ma hadari ne a […]
A halin da ake ciki dai labarin bazuwar cutar Ebola ya zama ruwan dare, lungu da sako duk ya shiga, wanda haka ya haddasa tsoro da zullumi a zukatan al’umma. Kasancewar daya daga hanyoyin daukar cutar shi ne hada jiki da mai cutar, wasu suna ganin yin musafaha ko gaisuwar hannu-da-hannu ma hadari ne a wannan zamanin. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko za ka iya daukar matakin daina irin wannan gaisuwar saboda tsoron wannan cuta ta Ebola? Ga ra’ayoyin wasu daga al’umma, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Bai kamata ba a daina – Murtala Rikadawa
Murtala rikadawa: “Bai dace ba kuma bai kamata ba saboda mutum ba zai iya kauce wa kaddara ba. Ai kamata ya yi mutum ya rika aiki da zihiri ba da badini ba. Idan ka ga a zihiri wanda za ka gaisa da shi ba shi da alamun cutar sai ka mika masa hannu ku gaisa amma kawai ka ki mika wa mutane hannu saboda wai kai kana gudun cutar Ebola gaskiya bai kamata ba.”