Ko za ka iya daina musafaha saboda tsoron cutar Ebola? 4
A halin da ake ciki dai labarin bazuwar cutar Ebola ya zama ruwan dare, lungu da sako duk ya shiga, wanda haka ya haddasa tsoro da zullumi a zukatan al’umma. Kasancewar daya daga hanyoyin daukar cutar shi ne hada jiki da mai cutar, wasu suna ganin yin musafaha ko gaisuwar hannu-da-hannu ma hadari ne a […]
A halin da ake ciki dai labarin bazuwar cutar Ebola ya zama ruwan dare, lungu da sako duk ya shiga, wanda haka ya haddasa tsoro da zullumi a zukatan al’umma. Kasancewar daya daga hanyoyin daukar cutar shi ne hada jiki da mai cutar, wasu suna ganin yin musafaha ko gaisuwar hannu-da-hannu ma hadari ne a wannan zamanin. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko za ka iya daukar matakin daina irin wannan gaisuwar saboda tsoron wannan cuta ta Ebola? Ga ra’ayoyin wasu daga al’umma, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Cutar ba za ta hana ni gaisuwa ba – Abdullahi Muhammad
Abdullahi Muhammad Jibril: “Ni ba zan daina gaisawa da mutane ba domin na san cewa yin haka ba zai sa in kamu da cutar ba. Kamar yadda masana suka fada mana cewa babu yadda za a yi mutum ya kamu da cutar Ebola ta yin musafaha har sai in ya yi musafaha da wanda cutar ta bayyana a jikinsa ko kuma ya yi hulda da dabbar da ke dauke da cutar kamar su birai da saursn namun daji. Saboda haka abin yi dai shi ne, mutum ya kula da tsaftar jikinsa da kuma na muhallinsa.