Ko za ka iya shiga motar da ba matuki?
Wani kamfanin kere-kere a Amurka ya kera wata mota, wacce ke sarrafa kanta, ba tare da matuki ba. A kwanakin bayan sun yi gwajin ta farko, inda ta samu matsala, ta yi hadari a kan hanya. Kamfanin ya sha alwashin sake gyara fasahar, domin kauce wa matsala. Abin tambaya a nan shi ne, idan an […]
Wani kamfanin kere-kere a Amurka ya kera wata mota, wacce ke sarrafa kanta, ba tare da matuki ba. A kwanakin bayan sun yi gwajin ta farko, inda ta samu matsala, ta yi hadari a kan hanya. Kamfanin ya sha alwashin sake gyara fasahar, domin kauce wa matsala. Abin tambaya a nan shi ne, idan an samar da irin wannan mota, ko za ka iya shiga, domin ta kai ka inda kake so? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana:
Ba zan shiga motar ba – dalha Albasu
Alhaji dalha Albasu: “A gaskiya ba zan taba yarda in shiga irin wannan motar ba, dalili kuwa shi ne, mota ma da direba tana yin hadari bare a ce babu direba? Ai wannan kasada ce, gaskiya ba zan yarda in taba shiga irin wannan mota ba. Duk nagartarta da kuma gyara kura-kuren baya da kamfanin ya ce ya yi, ai wannan sayar da rai ne; ba da ni ba, a nemi wani. Ta yaya ma mota babu direba ta san yadda za ta iya wuce ’yar uwarta ko kuma gane rami ko akwai kwana? Duk iya gyara da kawatata ba zan taba yarda in shiga cikin irin wannan mota ba.”
Ba da ni ba shiga motar – Ahmad Mukhtar
Alhaji Ahmad Muktar: “A’a, ba da ni ba, ban ma shiga motar da direbanta yake tukawa ba sai na tantance irin yadda yake tuki, na tantance natsuwarsa nake shiga mota ballantana a ce wannan ba ta da matuki? Ai duk iyakar gyara ko saita kuskuren baya da kamfanin ya ce ya yi, ba zan taba yarda in shiga irin wannan nmota ba. Mota da direba ma ya aka cika bare motar da babu direba? Wannan sai dai a kai jihohin Sakkwato da Zamfara, ni kam ba ni ba shiga irin wannan mota.”
Akwai matsala shiga motar – Ado Tukur
Ado M. Tukur: “Akwai matsala shiga motar da ba matuki, dalilna kuwa shi ne, idan matsuwa ta samu fasinja, wa zai gaya ma wa domin a tsaya ya biya bukatarsa. Dalili na biyu, shin za’a ware mata hanyar ta ce kamar yadda aka ware wa jirgin kasa ko kuwa zata shiga cikin cinkosan motocin da muke da su ne a hanya daya, a yi ta gwagwarmaya da kamar yadda ake yi da sauran motacin a hanya daya? Don haka ni ba zan shiga motar da ba matuki ba, domin akwai matsala.”
Akwai rashin natsuwa shiga motar -Ahmad Suleiman
Ahmad Suleiman Tudun Jukun: “Akwai rashin natsuwa shiga motar da ba matuki, sam ba zan shiga motar da ba matuki ba. Ya mutum ma da Allah Ya halitta, Ya ba shi natsuwa da kuma hankali wani lokaci sai ya aikata maka nau’in rashin natsuwa, ballantana na’urar da ba ta ji, ba ta ga ni kuma ba ta da hankali? Don haka ni ba zan shiga motar da ba matuki ba, ko nawa za a ba ni, domin akwai rashin natsuwa.”
Zan iya shiga wannan mota – Habibu Abubakar
Alhaji Habibu Abubakar: ‘’Ni zan iya shiga wannan mota da take tafiya ba tare da direba ba, a matsayina na dan Adam wanda yake tafiya da zamani, domin shi zamani na Allah ne. Ai motocin muke hawa a yanzu, a da babu su. Don haka ni a matsayina na mai tafiya da zamani, idan na ga wannan mota wadda take tafiya ba tare da direba ba, zan iya hawa. Ina mai tabbatar maka nan gaba ma, za a daina amfani da motocin da suke amfani da man fetur. Za a koma motocin da suke aiki da hasken rana da sauran na’urori iri-iri, domin haka zamani yake. Don haka ni a wurina, wannan ci gaba ne kuma zan iya hawa wannan mota idan na ganta.
Ba zan iya shiga motar ba – Buhari Zakari
Alhaji Buhari Zakari: ‘’Ni dai a yanzu ba zan amince na shiga wannan mota wadda take tafiya ba tare da direba ba. Dalilina kuwa shi ne, idan an ce wannan mota kwalta za ta hau, a gaskiya yanzu ba zan amince na shiga ta hau kwalta da ni ba. Domin idan aka ce wannan mota za ta hau kwalta ne to motocin da ke gabanta da motocin da ke bayanta su waye za su sarrafa su? Idan na’ura tana sarrafa wannan mota su kuma sauran motoci a nan matsala take, domin za su iya bugar wannan mota. Don haka ni ba zan shiga wannan mota ba a yanzu, sai dai zuwa nan gaba idan an kara inganta su suka yi yawa. To nan ya zama dole na shiga. Amma a yanzu ba zan shiga ba.”