Ko zaben kananan hukumin Jihar Kano zai sha bamban?
Ya zuwa yanzu Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano, wato KANSIEC ta tsayar da ranar 17 ga watan Mayun shekara mai zuwa, in Allah Ya kaimu ta zama ranar da za ta gudanar da zaben kananan Hukumomin jihar 44. A cikin wannan zabe da Hukumar ta KANSEIC, za ta gudanar za a zabi […]
Ya zuwa yanzu Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano, wato KANSIEC ta tsayar da ranar 17 ga watan Mayun shekara mai zuwa, in Allah Ya kaimu ta zama ranar da za ta gudanar da zaben kananan Hukumomin jihar 44. A cikin wannan zabe da Hukumar ta KANSEIC, za ta gudanar za a zabi shugabannin kananan Hukumomin jihar 44, da Kansiloli 484. Tun a ranar 17-11-2007, da Hukumar ta KANSIEC, ta yi zaben kananan Hukumomi, wadanda wa`adinsu ya kare a shekarar 2010, Majalisun kananan Hukumomin jihar suke karkashin tafiyarwar Kwamitocin riko.
Shugaban Hukumar ta KANSIEC, Dokta Sani Lawal Malumfashi, shi ya fada wa taron manema labarai aniyar Hukumarsa na gudanar da wannan zabe, a ranar Talatar makonda ya gabata a Kano, wannan zaben `yan siyasa da kungiyoyimasu radin kare dimokuradiyya da `yancin dan Adam da sauran mutanen jihar, musamman ma na karkara sun dade suna dakonsa.
Tsarin jadawalin zabubbukan da shugaban KANSEIC din yabayyana, zai fara aiki daga ranar 22 ga watan Janairun 2014,zuwa ranar zabubbukan wato 17 ga watan na Mayun badin. Ma`ana dai daga waccan rana ta 22-01-2014, Hukumar za ta fara busa usur dinta, alal misali daga wannan rana har zuwa ranar 10-02-2014, Hukumar za ta fayyace wa jam`iyyu tsarin yadda tsarin shirin zabubbukan za su kasance gaba daya. Jam`iyyu da `yantakara zasu fara yakin neman zabe daga ranar 16-02-2014, harzuwa tsakar daren wayewar garin ranar zabubbukan wato, 17-05- ga watan na Mayun, 2014.
Hukumar ta KANSIEC, ta tsaida tsakanin ranar 3 zuwa 13 gawatan Maris din badin su zama ranakun da Jam`iyyu za su gudanar da zabubbukan fitar da gwanayensu, da mika sunayen`yan takarar tasu. Hukumar zaben ta kuma kebe ranakun sayar da Fom su kasance tsakanin 14 zuwa 28 ga watan Maris 2014,ya yin da rana ta karshe wajen mayar da Fom din za ta kasance 4 ga watan Afrilu 2014.
Aikin tantance `yan takarar jam`iyyu da mika sunayenwakilan jam`iyyu da zasu tsare masu akwatuna a ranar zabubbukan, da batun fitar da sunayen `yan takarar da Hukumar Zaben ta amince su tsaya takarar da musanya sunayen `yan takara da fito da jerin sunayen `yan takara na karshe, Hukumarta KANSIEC ta kebe masu daga ranar 4 zuwa 25 ga watan Afril2014, kodayake kowane an ware masa wa`adinsa, amma dai ma`ana a cikin makonni uku duka za ta yi su, ya yin da ranar gudanar zabubbukan tana nan ranar 17 ga watan Mayu 2014.
Mai karatu kamar yadda na ambata ma a sama wadannan su ne wasu daga cikin jadawalin gudanar da zabubbukan kananan Hukumomin Jihar Kano, kananan Hukumomin da idan har Hukumar ta KANSIEC, ta cikasa alkawarinta yin zabubbukan a lokacin da ta kayyade, sun kasance shekaru kusan hudu ke nan batare da zababbun shugabanni ba, al`amarin da ko kusa ba ya taimakawa cikin tafiyar da Majalisun kananan Hukumomin, don kuwa abin da kundin tsarin mulki ya tanada shi ne a kodayaushe Majalisun kananan Hukumomi lallai suka san suna da zababbun shugabanni da `yan majalisun Dokokinsu, kamar yadda ake samu a gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.
Rashin samun hakan kuwa na faruwa ne daga irin yadda gwamnonin jihohin suke son su ci gaba da mallake kudaden shiga da ake turo wa Majalisun kananan hukumominsu, da kuma irin bukatar da suke da ita wajen ganin dukkan ayyukan da Majalisun za su gudanar, gwamnonin za su zabar masu koda kuwa ba irin wadannan ayyuka jama’a ke bukata ba, uwa uba kuma suna son lallai sai sun mallake shugabanni da kansilolin majalisu, wannan ke sa wa tun a lokacin tsayar da `yan takarar za ka taras wanda gwamnan jiha yake so, shi zai tsaya takara koda kuwa ta kansila ce, koda jama`a ba sa ra`ayinsa, kuma Hukumar zaben ta ce ya yi nasara.
Zabubbukan da Hukumar Zaben ta Jihar Kano za ta gudanar,su za su kasance wani zakaran gwajin dafi akan zabubbukan shekarar 2015, in Allah Ya kaimu tsakanin gwamnatin jihar da ke cikin tafiyar sabuwar PDP, amma da akidar Kwankwasiyya da `yan adawa masu jam`iyyar hadaka ta APC, duk kuwa da kasancewar Hukumomin Zabe na jihohi sun yi kaurin suna a kan jam`iyyar da ke mulki a jiha, ita ke lashe dukkan kujerun shugabanni da kansiloli a jihar, tsarin da ya zama tamfar yayi yau a kasa, ko a zabubbukan da aka gunadar a jihohi irinsuKwara da Ebonyi da sauransu a `yan kwanakin da suka gabata,jam`iyyar PDP da ke mulkin jihohin ita ta yi wa jam`iyyun adawa da suka shiga zabubbukan shal.
Amma zaben Majalisun kananan Hukumomi a Jihar Kano a lokacin gwamnatin ANPP ta Malam Ibrahim Shekarau,Hukumar Zaben ba ta yi zaben cinye dut ba. Alal misali, a zabubbukan kananan Hukumomi na karshe da Hukumar ta yi a ranar 17-11- 2007, babbar jam`iyyar adawa ta PDP a lokacin ta samu nasarar lashe kananan hukumomi uku, wato na Warawa da Dawakin Kudu da Kumbotso, kodayake ANPP ta samu karbe karamar hukumar Dawakin Kudu a kotu.
Kodayake a lokacin gwamnatin ta ANPP ta kasa gudanar da zabubbuka a Majalisun kananan hukumomin Albasu da Bichi da Madobi da kiru, akan abin da Hukumar zaben ta kira rashin matakan tsaro, abin da ya sa wadannan kananan hukumomi suka kasance a cikin rikon kwamitocin riko tun daga shekarar 2007, har zuwa 2011. da jam`iyyar PDP, ta zo kan karagar mulki.
Agefe daya ita ma jam`iyyar PDP, ta samu nasara a kotu a kan karamar hukumar Nassarawa, duk kuwa da kotun ta yanke hukunci bayan wa`adin shekaru uku da doka ta tanadar shugabannin kananan hukumomin jihar, don haka hukuncin kotun ya ce lallai gwamnati ta biya dan takarar PDP din albashi da alawus-alawus na tsawon shekaru uku da ya kamata ya kasance yana kan karagar mulki.
A zaman tabbatar da sahihi kuma ingantaccen zabe shugaban hukumar ta KANSIEC, Dokta Malumfashi ya tabbatar wa da jam`iyyun da al`ummar jihar cewa Hukumarsa za ta tanadar da bin dukkan sharudda da ka`idojin zabubbukan don ta kai ga nasara, amma ya tunatar da `yan siyasar cewa su ma su bada ta su gudummuwar wajen tabbatar da aiki da dokoki da sharuddan zabubbukan, don a fadarsa ba wai hukumar kadai ke da alhakin tabbatar da sahihanci da ingantaccen zabe ba. Don haka abin jira a gani ko zaben na Jihar Kano a wannan karon zai sha bamban.