Ko zai yiwu a rika yanke wa barayin gwamnati hukuncin kisa?

kungiyar kwadago a Najeriya ta ba da shawarar a rika yanke wa duk wani jami’in gwamnati da aka kama da laifin satar dukiyar gwamnati hukuncin kisa. Abin tambaya a nan shi ne, ko zai yiwu a rika yin haka a Najeriya? Ga abin da mutane suka bayyana a kan haka: Hukuncin ba zai yiwu ba […]

Ko zai yiwu a rika yanke wa barayin gwamnati hukuncin kisa?
Ko zai yiwu a rika yanke wa barayin gwamnati hukuncin kisa?

kungiyar kwadago a Najeriya ta ba da shawarar a rika yanke wa duk wani jami’in gwamnati da aka kama da laifin satar dukiyar gwamnati hukuncin kisa. Abin tambaya a nan shi ne, ko zai yiwu a rika yin haka a Najeriya? Ga abin da mutane suka bayyana a kan haka:

Hukuncin ba zai yiwu ba – Dandin Mahe

Adam Umar, a Abuja

Bello Dandin Mahe Suleja: “A gaskiya aiwatar da wannan hukunci ba zai yiwu a kasar nan ba. Dalili kuwa shi ne, son kai irin na shugabanninmu wadanda burin kowa idan ya samu mulki shi ne ramakon gayya, inda a karshe sai ya kai ga aiwatar da hukuncin a kan wanda bai aikata al’amarin ba. Ga kuma matsalar bambance-bambancen kabilanci da na addini da na yanki, ta yadda idan aka yi hukuncin, al’ummar wadanda aka zartar da hukuncin a kansu suna iya danganta lamarin ta wannan bangare har ya kai ga haifar da tashin hankali.”

Hukuncin kisa ba zai yiwu ba – Usman Adamu

John Wada, a Lafiya

Alhaji Usman Adamu: “Ni dai ra’ayi na shi ne, a ci gaba da tuhumar wadannan mutane da suka sace dukiyar kasar nan su dawo da su ko ba duka ba. Idan sun ki kuma sai a buga sunayensu a jaridu a kuma sanar a dukkan gidajen radiyon kasar nan kowa ya sani cewa su suka sace dukiyoyin kasar nan, saboda haka sun ci amanar kasa dole a wulakanta su komai matsayinsu. Ban goyi bayan a yanke musu hukuncin kisa ba. A dai wulakantasu ta wadannan hanyoyi da na bayyana idan sun ki dawowa da abubuwa da suka sace, don ya kasance darasi ga wadanda ke niyyar yin haka. Na tabbata ta haka ne za a magance lamarin a kasar nan.”

Hukuncin ba zai dace ba – dahiru Dauda

Adam Umar, a Abuja

dahiru Dauda Bindawa: “daurin rai da rai ya kamata a yi musa ba hukuncin kisa ba. Duk da cewa satar kudin gwamnati tamkar aikata kisan kai ne a kan al’umma kasancewar yin hakan nasa a rasa rai a hatsarin hanya a sakamakon kwashe kudin da aka ware don yin titi ko samar da magunguna a asibiti da dai sauransu, ni a ra’ayina daure barayin ya kamata a yi na rai-da-rai ba kasha su ba. Dalili kuwa shi ne, tsarinmu ya bambanta da na China. Bai kamata ba kuma mu dauko wata doka da suke yi ba, musamman irin wannan mai tsanani.”

Tsarin ba zai yiwu ba a Najeriya – Muhammad Soja

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Muhammad Hussaini Soja: “Ni a nawa ganin batun a yanke hukuncin kisa da kungiyar kwadago ta yi ga duk wasu barayin gwamnati hakan ya yi tsamari. Dalilina kuwa shi ne, maimakon a yanke hukuncin kisa ga barayin na gwamnati, kamata ya yi a ce a yanke musu hukuncin daurin-rai-da-rai. Domin ai in an yanke musu hukuncin kisa babu yiwuwar su canza daga wannan mummunan hali na kuruciyar bera amma in aka ce daurin-rai-da-rai ne mai yiwuwa wata ran za su iya fitowa ta yadda nadama za ta iya amfani.”

Za a iya yin haka a Najeriya – Muhammad Hussaini

John Wada, a Lafiya

Alhaji Muhammad Hussaini: “Nawa ra’ayi a wannan batu shi ne, zai iya yuwa a aiwatar da wannan doka wato ta hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar dukiyar kasar nan muddin ’yan Majalisar Tarayya sun shigar da ita a doka. Kuma ina goyon bayan wannan yanke hukuncin kisa ga duk wanda ya sace dukiyar kasar nan har in za a gudanar da haka. Don ba shakka idan ana yin haka, wadannan mutane za su daina. Haka su ma wadanda ke niyyar yin haka za su ji tsoro. Ai kamar yadda ka sani, ba sabuwar doka ba ce, ana aiwatar da wannan doka a wasu kasashen waje kamar su China da sauransu. Shi ya sa idan ka tafi wadannan kasashe za ka ga lamarin da sauki ba kamar yadda yake a nan Najeriya ba.”

Tsarin zai yiwu a Najeriya – Alhaji Ibrahim

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Alhaji Ibrahim Mai Shago: “A ganina, hukuncin kisa da kungiyar kwdago ta ba da shawarar a zartar ga barayin gwamnati, hakan ya yi daidai. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, ai wadannan mutane wato barayin gwamnati su ma ai kashe jama’a suka yi, kasancewar sun jefa al’ummar kasa cikin halin ni ’ya su. Don haka hukuncin kisa shi ya fi da a bar su, domin in an bar su za su iya dawowa su sake aikata irin wannan hali na rashin tausayi.”