Ko zai yiwu Buhari ya yi raba daidai a mukamansa tsakanin Arewa da Kudu?

Tuni dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara nada mukarraban gwamnatinsa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko shugaban zai iya yin raba daidai tsakanin yankunan Arewa da Kudu a nade-naden mukarraban gwamnatin tasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Zai yi wuya a daidata rabon mukamai  – […]

Ko zai yiwu Buhari ya yi raba daidai a mukamansa tsakanin Arewa da Kudu?
Ko zai yiwu Buhari ya yi raba daidai a mukamansa tsakanin Arewa da Kudu?

Tuni dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara nada mukarraban gwamnatinsa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko shugaban zai iya yin raba daidai tsakanin yankunan Arewa da Kudu a nade-naden mukarraban gwamnatin tasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Zai yi wuya a daidata rabon mukamai  – Kana Mainama

Abubakar Haruna, a Abuja

Kana Mainama: “Ni a ganina, zai yi wuya Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya daidata rabon mukamansa tsakanin yankin Kudu da Arewa saboda abin da ya kamata a ce ya yi ke nan don kowa nasa ne, da wanda bai zabe shi ba da wanda ya zabe shi; Musulmi ne shi ko Kirista duk ’yan Najeriya ne.”

Ba za a iya samun daidaito ba – Garba Hashimu

Shu’aibu Ibrahim, a Gusau

Garba Hashimu: “Ni ra’ayina shi ne, ba za a samu daidaito ba saboda tun da ya ce cancanta za a bi, to zai yi wahala tunda ko su masu ba da sunayen suna shakkar sunayen wadanda suke bayarwa saboda ba su da aminci da gaskiyarsu, don suna da kashi a jika. Saboda yanzu kam sai abin da jama’a suka gani kawai amma babu maganar daidaito.”

Buhari ya duba cancanta kawai– Muhammadu Ahmadu

Abubakar Haruna, a Abuja

Muhammadu Ahmadu: “Ba zai yiwu Shugaba Buhari ya daidata rabon mukamansa tsakanin mutanen Kudu da Arewa saboda shi Buhari cancanta yake dubawa ba bangaren da mutum ya fito ba. Abu na biyu shi ne, ai mun fi mutanen Kudu yawa saboda haka babu yadda za a yi kasonmu ya zama daya daidai-wa-daida.”

Zai iya daidaitawa – Zubairu Sham’una

Muhammad Yaba, Kaduna

Zubairu Shan’una: “Gaskiya ina ganin Shugaban kasa zai iya daidaita rabon mukamai, domin adalci amma sai dai akwai bukatar mu tuna cewa a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Jonathan, ai shi ma ya damka duk tattalin arzikin kasar nan ne a hannun mutanen yankinsa. Amma dai tun da fadar Shugaban kasa sun ce za a gyara, ina ganin za su daidata mukamin domin kowa ya ji dadi.”

Zai iya daidaita mukaman – Ibrahim Sa’idu

Shu’aibu Ibrahim, a Gusau

Ibrahim Sa’idu Abdullahi: “Ni a ra’ayina, Shugaban kasa Muhammad Buhari zai iya daidaita rabon mukamai saboda ya ce za a bi cancanta ne ba suna ko jam’iyya ko kuma a dubi wanda ya ba da sunanka ba. Don haka idan ka ga ba a daidaita ba, to ba a samu wadanda suka dace ba daga yankinku na Arewa ko Kudu.”

Ya dace a daidaita – Haruna Mika’ilu

Muhammad Yaba, a Kaduna

Malam Haruna Mika’ilu: “Ya dace mana, domin kada a yi son kai, kowa a ba shi hakkinsa a matsayinsa na dan kasa. Sai dai kuma a zabi mutane nakwarai masu gaskiya koda daga wane yanki suka fito, domin ba su mukamai. Kada a zabar mana bara-gurbi. Tun da Shugaban kasarmu mai gaskiya ne da rikon amana, shi ya sa muke son a zabar mana mutanen kwarai a ba su mukamai.”