Kocin Brazil Dunga ya koka da filin wasan Amurka
Sabon kocin kasar Brazil Dunga ya bayyana rashin gamsuwa da yadda filin wasa mai suna MetLife Stadium a Amurka ya kasance a lokacin da kasarsa Brazil ta fafata da ta Ekuador a wasan sada zumunta da ya gudana a ranar Talatar da ta wuce.A wasan, Brazil ce ta yi nasara da ci 1-0 bayan dan […]
Sabon kocin kasar Brazil Dunga ya bayyana rashin gamsuwa da yadda filin wasa mai suna MetLife Stadium a Amurka ya kasance a lokacin da kasarsa Brazil ta fafata da ta Ekuador a wasan sada zumunta da ya gudana a ranar Talatar da ta wuce.
A wasan, Brazil ce ta yi nasara da ci 1-0 bayan dan kwallon Brazil mai suna Willian ya zura kwallo daya tilo da ta ba Brazil nasara a wasan.
Dunga ya ce kafin kasashen biyu su fafata a wasan sai da ’yan wasan zari-ruga na Amurka suka yi amfani da filin da hakan ta sa filin ya yi kaca-kaca kuma ya hana kwallo gudu.
Kocin ya ce yana da tabbacin haka ne ta sa ’yan kwallon gabansa suka kasa samun sukunin zura kwallaye da yawa a ragar Ekuador.
Ya zuwa yanzu, kocin ya lashe wa Brazil wasannin sada zumunta biyu a jere bayan ya samu nasara a kan Kolombiya da ci 1 mai ban haushi a ranar Juma’ar da ta wuce.
Brazil dai ta kori tsohon kocinta Luis Scolari ne tun bayan da kasar Jamus ta yi kaca-kaca da ita a gasar cin kofin duniya da ya gabata a matakin Semi-Fainal inda aka tashi wasa 7-1.