Kocin Dortmund zai ajiye aiki
Kocin kulob din Borussia Dortmund da ke Jamus Jurgen Kloop a shekaranjiya Larabai cewa ya fadawa manema labarai cewa ya yanke shawarar barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana. Sai dai kocin ya ce hakan ba yana nufin ya bar harkar horarwa ba ne zai nemi wani kulob don ya cigaba da horarwa […]
Kocin kulob din Borussia Dortmund da ke Jamus Jurgen Kloop a shekaranjiya Larabai cewa ya fadawa manema labarai cewa ya yanke shawarar barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana. Sai dai kocin ya ce hakan ba yana nufin ya bar harkar horarwa ba ne zai nemi wani kulob don ya cigaba da horarwa a can walau a Jamus ko kuma a wata kasa daban.
Jurgen Kloop shi ne kocin da ya kafa tarihin lashewa kulob din gasar rukuni-rukuni na Jamus sau biyu a jere watau a shekarar 2011 da kuma a 2012 baya ga hayewa da kulob din matakin karshe a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Tutrai (UEFA Champions League) a shekarar 2013.
Kocin ya tabbatar da cewa da zarar ya bar kulob din Dortmund zai fara aiki ne a wani kulob daban wanda bai ambata ba.