Kocin Super Eagles Jose Paseiro ya yi murabus
Peseiro ya yi murabus bayan shafe watanni 22 yana horas da tawagar Super Eagles.
Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Jose Peserio ya sanar da murabus daga mukaminsa.
Sanarwar na ƙunshe ne cikin wani saƙo da kociyan dan kasar Portugal ya wallafa a shafinsa na X.
- Fursunoni na zanga-zanga saboda ƙarancin abinci a gidan yari
- Kalaman tunzuri yayin wa’azi na haddasa kiyayya — Izala
A cewar saƙon da Peseiro ya wallafa, “a jiya muka kawo ƙarshen kwantiragin da ke tsakanina da Hukumar Kwallon ƙafa ta Najeriya NFF.
“Abin farin ciki da alfahari ne horar da tawagar Super Eagles. Watanni 22 kenan da muka kwashe muna wannan sadaukarwa da matuƙar sha’awar aikin.
“Muna jin mun yi abin da ya kamata,” kamar yadda kocin ya wallafa a shafinsa na X.
Peseiro ya miƙa godiya ga shugabannin Hukumar Kwallon Kafar Nijeriya (NFF) na baya-bayanan da mai ci wato Amaju Pinnick da Ibrahim Gusau, Babban Sakataren Hukumar, Mohammed Sanusi da Sakatare Dayo Enebi.
Ya kuma nuna godiyarsa ga ’yan wasa da ma’aikatan tawagar da suka mara masa baya a watani 22 da ya horar da ’yan wasan tawagar.
Murabus ɗin Peseiro dai na zuwa ne bayan ya ja ragamar horas da ’yan wasan tawagar Super Eagles a Gasar Kofin Nahiyyar Afirka ta AFCON wadda ta sha kashi a wasan ƙarshe da ta fafata da mai masaukin baki Ivory Coast.
Bayanai sun ce Hukumar NFF na tattaunawa kan sabunta kwantiragin kocin amma maganar ta zagwanye ƙarshen watan Fabarairun da ya gabata.