Kofin Aisha Buhari: Ko karshen mulkin Najeriya a kwallon mata ya zo ne?

’Yan wasan Afirka ta Kudu sun lallasa Najeriya da ci hudu da biyu.

Kofin Aisha Buhari: Ko karshen mulkin Najeriya a kwallon mata ya zo ne?

A ranar Talata da ta gabata ce ’yan wasan kwallon kafa na Afirka ta Kudu na mata, Bayana Bayana suka lallasa Super Falcons ta Najeriya da ci hudu da biyu a wasan karshe a gasar cin Kofin Aisha Buhari na farko.

An buga wasan ne a filin wasa na Mobolaji Johnson da ke Onikan a Jihar Legas.

Tun a minti shida da fara wasan ne ’yar wasan bayan Najeriya Alozie Michelle ta ci gida, sannan Enome Ebi, wadda fitacciyar ’yar wasan Super Falcons ce ta taba kwallo da hannu a gidan Najeriya, inda ’yar wasa Bayana Bayana Motlhalo Linda ta jefa kwallon a ragar Najeriya a bugun fenariti.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci Salgado Gabriels ta kara kwallo na uku a ragar Najeriya.

Da aka dawo hutun rabin lokaci ne ’yar wasan Najeriya Ikechukwu Vivian ta farke kwallo biyu, sai murna ta koma ciki inda kwatsam Afirka ta Kudu da sake samun fanareti, inda ta ci kwallo na hudu.

A watan Oktoba ne Najeriya za ta buga wasanta na gaba na neman gurbin shiga gasar cin Kofin Afirka na mata, inda za ta fafata da Ghana.

– Najeriya ta dade tana ‘mulki’ a wasan mata na Afirka

Sai dai lamarin ya zo da ba-zata, kasancewar ana kallon ’yan wasan Najeriya mata a matsayin zakaran gwajin dafi a duk lokacin da ake batun kwallon kafa na mata a Afirka.

Misali, a Gasar Kofin Afirka na mata da aka buga guda 13, Najeriya ce ta lashe guda 11.

An fara gasar ce daga shekarar 1991 sannan zuwa yanzu an buga gasar sau 13.

Na karshe shi ne na shekarar 2018 da Najeriya da doke Afirka ta Kudu a wasan karshe a bugun fanareti.

Daga cikin 13 da aka fafata, Najeriya ta lashe sau 11 a shekarun 1991 da 1995 da 1998 da 2000 da 2002 da 2004 da 2006 da 2010 da 2014 da 2016, da kuma na karshe da aka buga a shekarar 2018.

A bara ya kamata a buga gasar, amma aka dakatar saboda bullar annobar COVID-19 da ya addabi duniya a lokacin.

Baya ga lashe guda 11, a guda biyun da Najeriya ba ta lashe ba, ita ce ta zo ta uku a gasar ta shekarar 2008, sannan ta zo ta hudu a gasar ta shekarar 2012.

– Zaratan ’yan wasa

A bangaren zaratan ’yan wasa kuwa ba a magana, domin a duniyar kwallon mata a Afirka, Najeriya ce kan gaba wajen zaratan ’yan wasa mata.

Tun farkon gasar Gwarzuwar ’Yar Wasan Afirka Mata zuwa yanzu, an yi gasar sau 17, kuma a cikin 16 da aka yi ’yan wasan Najeriya ne suka lashe 11.

’Yar wasan Najeriya da Barcelona, Asisat Oshoala ce ta lashe kyautar ta karshe a shekarar 2019, sannan kafin nan ta lashe guda uku a shekarun 2014, da 2016 da kuma 2017.

Sai tsohuwar ’yar wasar Najeriya, Perpetua Nkwocha da ita ma ta lashe kyautar sau hudu a shekarun 2004, da 2005, da 2010 da kuma 2011.

Cynthia Uwak ta lashe sau biyu a shekarun 2006 da 2007, sai tsohuwar ’yar wasan Najeriya, wadda kusan da ita ake koyi a kwallon mata a Najeriya, Mercy Akide, wadda ta lashe kyautar ta farko a shekarar 2001

Wadda ta lashe Gwarzuwar Kwallon Mata ta Afirka ta farko Mercy Akide Hoto: vanguard.com
– Dalilin da Super Falcons ke samun koma baya

Wasu masu kallon kafa suna ganin ko matan sun fara zama kamar mazan ne wato Super Eagles — tawagar da aka dade ana zarga rashin kishin kasa.

Misali Rasheedat Ajibade, wadda ita ce fitacciyar ’yar wasan tsakiya da Najeriya ke ji da ita a yanzu kuma take laka leda a kungiyar Atletico Madrid, kusa da fara gasar ce ta fito ta bayyana cewa ba za ta samu zuwa gasar ba saboda rauni da ta ji a atisaye a Spain.

Haka kuma kwazon da suke nunawa a wasa ya yi rauni. Misali a wasan karshe na gasar cin Kofin Afirka na karshe da kasar ta lashe, sai da aka kai bugun fanareti, sannan suka sha da kyar, ba kamar yadda suka saba lallasa kasashe ba a baya.

Zaratan ’yan wasan irinsu Asisat Oshoala, wadda kusan yanzu za a iya cewa tana cikin masu daukar nauyin kungiyar Barcelona, ba ta nuna kwazo ba sosai a gasar.

Haka ma Franciska Ordega, wadda ta fi nishadantar da masu kallo abin ya koma baya.

A wasan karshe na Kofin Aisha Buhari, Enome Ebi ce ta jawo fanareti biyu, wanda da alamu ko dai shekaru ne suka sa jikinta ya yi sanyi, ko kuma rashin kishin, duba yanayin kwarewarta a buga baya.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara