Kofin Duniya: Jamus ta lallasa Curaçao da ci 7 a wasan farko
Jamus ta fara gasar da ƙafar dama, yayin da ta zama ƙasa ta farko da ta zazzaga ƙwallaye masu yawa.
Ƙasar Jamus ta fara gasar Kofin Duniya da gagarumar nasara bayan ta doke Curaçao da ci 7-1 a wasan rukunin E da aka buga a Houston.
Tun da farko, Felix Nmecha ne, ya fara zura wa Jamus ƙwallo.
- Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe
- Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno
Sai dai Curaçao ta ba da mamaki lokacin da Livano Comenencia ya zura mata ƙwallo a minti na 21, wadda ta zama ƙwallo ta farko da ƙasar ta taɓa ci a tarihin gasar Kofin Duniya.
Sai dai farin cikin Curaçao ya gushe, domin Jamus ta ƙara mata ƙwallo a raga ta hannun ɗan wasan bayanta Nico Schlotterbeck.
Kafin tafiya hutun rabin lokaci Kai Havertz ya ƙara ƙwallo ta uku daga bugun fenariti.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Jamus ta ci gaba da nuna ƙwarewa inda Jamal Musiala, Nathaniel Brown da Deniz Undav suka ƙara wasu ƙwallaye, yayin da Havertz ya sake zura ƙwallonsa ta biyu.
Jamus ta tafi da maki uku da kuma ƙwallaye masu yawa, yayin da Curaçao ta bar filin tana murnar kafa tarihi da ƙwallonta ta farko a Gasar Kofin Duniya.