Kofin Duniya: ’Yan wasan cikin gida 8 da Super Eagles ta gayyata

Emmanuel Onyebuchi dan wasan baya da yake taka leda a Kungiyar Rangers International FC da ke Jihar Enugu.

Kofin Duniya: ’Yan wasan cikin gida 8 da Super Eagles ta gayyata

Tawagar Kwallon Kafa ta Super Eagles ta Nijeriya ta gayyaci sababbin ’yan kwallo takwas da za su wakilci kasar domin buga mata wasannin neman gurbin shiga Gasar Kofin Duniya na 2026.

Tuni Super Eagles karkashin jagorancin sabon mai horaswa Eric Chelle, ta fitar da jadawalin ’yan wasa na farko da za su taka mata leda a wasannin neman gurbin da za ta take a watan Maris din nan da muke ciki.

Daga cikin sababbin ’yan wasan da ta gayyato da ba su taba wakiltar Nijeriya ba, har da irin su Papa Mustapha da Ifeanyi Emmanuel Onyebuchi da Christantus Uche da Akor Adams da Tolu Arokodare da Igoh Ogbu da Anthony Dennis da Kayode Bankole.

A ranar 26 ga watan Maris ɗin nan Super Eagles za ta je birnin Kigali domin fafatawa da tawagar ’yan wasan ƙasar Rwanda.

Ranar 25 kuma za ta goge raini tsakanin ta da Zimbabwe a nan gida Nijeriya a Filin Wasa na Godswill Akpabio da ke garin Uyo, Jihar Akwa Ibom.

Eric ya gayyato Ahmed Musa

Abin da ya ɗauki hankalin mutane a jerin ’yan wasan da Super Eagles ta fitar shi ne yadda a wannan lokacin ta gayyato ’yan wasan da suke taka leda a gasar Firimiya ta cikin gida su wakilci kasar.

Cikin ’yan wasa na cikin gidan har da tsohon Kyaftin din tawagar, Ahmad Musa, wanda tun bayan komawarsa Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars a farkon shekarar 2024, bai sake samun gayyata daga Super Eagles ba sai wannan karon.

Papa: Daga cikin ’yan wasan da aka gayyato a nan gida Nijeriya akwai irinsu Papa Mustapha Daniel, dan wasan tsakiya da ke taka leda a Kungiyar Niger Tornados da ke birnin Minna na Jihar Neja.

Matashin mai shekara 23 dan Jihar Legas, kuma ya koma taka leda ne a kungiyar Niger Tornados a watan Agustan shekarar 2024.

Kafin ya koma Niger Tornados, ya taka leda a Kungiyar Adanaspor da kasar Turkiyya, sannan ya wakilci tawagar ’yan Najeriya masu taka leda a cikin gida.

Onyebuchi: Sai kuma Emmanuel Onyebuchi dan wasan baya da yake taka leda a Kungiyar Rangers International FC da ke Jihar Enugu.

Matashin dan wasan mai shekara 24 mazaunin Jihar Kaduna ne, inda ya fara buga kwallo.

Ya kuma taka leda a kungiyoyin Plateau United da MFM FC da FC Shkupi da ke kasar Macedonia ta Arewa kafin ya koma Rangers.

Bankole: Akwai kuma Kayode Bankole na Remo Stars, mai shekaru 22, wanda matashin mai tsaron gida ne da ke tashe a Gasar Firimiya ta Nijeriya.

Matashin golan ya fara tsaron gidan Kungiyar Remo ne a kakar shekarar 2020. Kafin nan ya tsare ragar Kungiyar Shooting Stars a kakar 2019 zuwa 2020.

Kayode Bankole haifaffen garin Ipokia ne da ke Jihar Ogun.

Ahmed Musa: Sai kuma wanda aka fi mayar da hankali a kansa, Ahmed Musa, wanda Kyaftin ne na tawagar ta Super Eagles, amma ya dade ba ta gayyace shi ba, lamarin da ake tunanin ko dai don ya koma Firimiyar Nijeriya ne da taka leda.

Tsawon lokaci an yi ta jiran ganin ko sabon kocin Super Eagles, zai gayyace shi.

Yanzu dai fitaccen dan wasan, wanda yanzu yake Kungiyar Kano Pillars, ya samu shiga cikin jerin ’yan wasa na farko da kocin ya fitar.

Ahmed Musa dai ya buga wa Nijeriya kwallo sau 110, inda ya fi kowane ɗan ƙwallo wakiltar ƙasar.

A yanzu dai tawagar ta Super Eagles tana mataki na 5 da maki 3 ne a Rukunin C, lamarin da ya sa take neman nasara a wasanninta da Rwanda da kuma Zimbabwe, don samun gurbi a Gasar Kofin Duniya da za a yi a baɗi.