‘Kofin Madara’

Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne a kan “kofin madara”. Labarin ya kunshi yadda kyautatawa ke da matukar amfani a rayuwa. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi.   Bello yaro ne dan kankani wanda iyayensa suka rasu ba tare da sun bar […]

‘Kofin Madara’

Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne a kan “kofin madara”. Labarin ya kunshi yadda kyautatawa ke da matukar amfani a rayuwa. A sha karatu lafiya.

Taku; Amina Abdullahi.

 

Bello yaro ne dan kankani wanda iyayensa suka rasu ba tare da sun bar masa gado ba. Samun abinci yana matukar yi masa wahala. Sai ya yanke shawarar samarwa kansa sana’ar hannu da zai rika samun na abinci.

Ran nan kishin ruwa ya dame shi, ya zagaya duk inda zai ga ruwa amma bai samu ba.  Sai ya nufi wani babban gida da aka kawata shi da furanni ya kwankwasa kofar. Ana budewa sai ya ga wata wata yarinya wacce shekaranta ba ta fi nasa ba. Ya roketa da ta ba shi ruwa ya sha. Koda ta tafi dauko ruwa, da ta dawo sai Bello ya yi mamakin ganin Kofi babba cike da madara tac e ya sha domin daga ganinsa an san yunwa yake ji. Ya gode mata ya yi tafiyarsa.

Bayan shekaru masu yawa, sai yarinyar ta kwanta rashin lafiya. A nan aka samu wani likita wanda shi kadai ya iya gano abin da ke damunta amma kudin aikin akwai tsada.  Bayan an yi mata aikin ta farfado kuma ta samu lafiya ne sai ta nemi jin wanda ya dauki nauyin yi mata aikin, tun da a lokacin iyayenta sun talauce ba za su iya biyan kudin aikin ba. 

Da ta tambaya Likitan nawa ne kudin aikin kuma wa ya biya mata sai ya ce mata ai ta riga ta biya tun shekaru da dama da suka wuce da kofin madara.  Ya tuna mata yadda ta taimake shi da kofin madara a lokacin da yake jin kishi a lokacin suna yara.

Da fatan Manyan gobe sun dauki darasi daga wannan labari.