Kofur ya bindige ASP a Yobe
A ranar Juma’ar makon jiya ta ne wani Kofur din ’yan sanda mai suna Bitrus Androw da ake kira da Kwaba ya bindige wani dan sanda mai mukamin ASP mai suna Olesoje Elegbede a babban ofishin ’yan sanda na hanyar Nguru cikin garin Gashuwa ta Jihar Yobe.Wata majiya mai tushe ta bayyana wa Aminiya cewa […]
A ranar Juma’ar makon jiya ta ne wani Kofur din ’yan sanda mai suna Bitrus Androw da ake kira da Kwaba ya bindige wani dan sanda mai mukamin ASP mai suna Olesoje Elegbede a babban ofishin ’yan sanda na hanyar Nguru cikin garin Gashuwa ta Jihar Yobe.
Wata majiya mai tushe ta bayyana wa Aminiya cewa Kofur Kwabba ya bindige maigidansa ne bayan ya kawo karar wata farkarsa a ofishinsu, Da yake ranar DPO baya gari ASP Elebede ne mai kula da ofishin inda ya sa aka nemo farkar domin jin me ke faruwa. Majiyar ta ce yayin da aka nemi bayani daga Kofur Kwaba a kan kararsa, sai ya kasa kawo dailila, hakan ne ya sa babban jami’in ya umarci matar ta tafi.
Majiyar ta ce”Lokacin da ASP Elegbede ya umurci yarinyar ta yi tafiyarta; sai Bitrus Kwaba yayi barazanar zai harbe ta a gaban ofishin, inda ta koma cikin ofishin da gudu.
Ganin haka sai ASP Elegbede ya tsawata masa cewa a nan za ka harbi mutum, kuma ya ce zai rubuta takardar ladabtarwa a kan ya nuna rashin da’a da saba wa ka’idar aiki.
Majiyar ta ce sai Kofur Kwaba ya dubi babban jami’in lokacin da yake sunkuye yana rubuta takardar ya narka masa bindiga harbi biyar, nan take ya fadi kasa, sai aka garzaya da shi babban asibitin Gashuwa inda rai ya yi halinsa.
’Yan sandan na Gashuwa sun kama wanda ake zargin inda suka kai shi Damaturu babban ofishinsu don daukar mataki a kai.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe Sunusi Ahmed Rufa’i ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce rashin jin dadin hukuncin marigayin ya yi ne ya sa Kofur Bitrus ya bindige ASP Elegbede. Ya ce sun dukufa kan bincikar gaskiyar matsalar.