Kogi ya ci ɗan shekara 55 a Jigawa

Wani mutum mai shekaru 55 ya rasu bayan da ya je yin wanka a  bakin kogi a yankin Hadejia da ke Jihar Jigawa.

Kogi ya ci ɗan shekara 55 a Jigawa

Wani mutum mai shekaru 55 ya rasu bayan da ya je yin wanka a  bakin kogi a yankin Hadejia da ke Jihar Jigawa.

Kakakin Rundunar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Jigawa, Badaruddeen Tijjani, ya ce mutumin ya cimma sa’a ne a ranar Asabar da safe.

Ya ce, “Malam Sulaiman Potiskum mai shekaru 55 ya rasu ne a wani rafi da ke yankin Gada, Bakin Kogi a Ƙaramar Hukumar Hadejia.

“Ajali ya cim masa ne a lokacin da yake wanka a bakin kogin, amma aka yi raahin dace, igiyar ruwa ta wuce da shi.”

Tijjani ya ce daga bisani masu aikin ceto suka gano gawar, kuma likitoci a Babban Asibitin Hadejia sun tabbatar da rasuwarsa.

Jami’in ya ce an miƙa gawar ga iyalan mamacin, sannan ya shawarci masunta da sauran jama’a da su haƙura da zuwa yin su ko wanka a bakin kogi, saboda ƙarfin ruwan, a sakamakon ambaliyar ruwan sama.

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo