Kogi ya ci dalibai biyu a Jihar Nasarawa
Kogin Uke da ke karamar Hukumar Karu a hanyar Masaka zuwa Keffi a Jihar Nasarawa ya ci wasu daliban makarantan sakandare biyu a yankin a makon jiya. Lamarin ya auku ne da safe lokacin da daliban biyu dukansu maza suka bar makarantarsu zuwa kogin wanda ba shi da nisa daga makarantar don yin wanka inda […]
Kogin Uke da ke karamar Hukumar Karu a hanyar Masaka zuwa Keffi a Jihar Nasarawa ya ci wasu daliban makarantan sakandare biyu a yankin a makon jiya. Lamarin ya auku ne da safe lokacin da daliban biyu dukansu maza suka bar makarantarsu zuwa kogin wanda ba shi da nisa daga makarantar don yin wanka inda suka gamu da ajalinsu.
Wakilinmu wanda ya ziyarci yankin ya gana da Sarkin Uke, Alhaji Bako Muhammed, kan lamarin inda ya ce, “daliban biyu sun tafi kogin ne don yin wanka kamar yadda suka saba. Da ruwan kogin ya soma jan daya daga cikinsu sai na biyun ya yi yunkurin ceto shi, amma sai shi ma ruwan ya nutse da shi. Kogin ya cika makil da ruwa ’yan kwanakin nan. Mun dade muna gargadin al’ummar yankin cewa su daina shiga kogin don kauce wa hadarin da ke tattare da hakan,” inji Sarkin.
Daga nan sai Sarkin ya yi amfani da wannan damar inda ya karyata jita-jitar da wasu mutane a jihar ke yadawa cewa al’ummar yankin ne ke kashe mutane a kogin, ya ce kowa a duniya na da irin nasa ajalin. A cewarsa daliban da kogin ya halaka da sauran da suka rasu a kogin a baya, sun gamu ne da ajalinsu ne a wurin saboda haka Allah Ya hukunta. Saboda haka ya nemi mutane su yi watsi da wannan jita-jita. Zuwa lokacin rubuta wannan rahoto Aminiya ta samu labarin an gano gawar daya daga cikin daliban, yayin da ake ci gaba da neman gawar na biyun.
Wani magidanci a yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa “Wannan mugun kogi ya halaka daliban ne da rana. Kuma abin da ya ba ni mamaki shi ne ba wai an yi ruwan sama ne a nan ba. An wayi gari ne kawai sai aka tarar kogin ya cika makil da ruwa. Mutane da dama da ke wannan yanki da suka san kogin sun yi ta fargaba sakamakon haka. A ranar Litinin ce muka samu labarin cewa wasu dalibai biyu sun rasa rayukansu a cikinsa.” Ya ce shi kansa ya taba rasa dansa mai shekara 24 a kogin a kwanakin baya.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi ofishin ’yan sandan da ke yankin don jin ta bakinsu game da lamarin, sun ce har zuwa lokacin ba a kai musu rahoton aukuwar lamarin ba.