Kogi ya ci mutum uku a Jihar Bauchi

Mutum uku ne ruwa ya ci a Kogin Kirfi da ke Karamar Hukumar Kirfi, a Jihar Bauchi. Shugaban Karamar Hukumar Kirfi, Alhaji Abdu Danmalikin Bara ne ya sanar da haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, inda ya ce mutanen sun rasu ne lokacin da ruwa ya yi ambaliya, su kuma suka […]

Kogi ya ci mutum uku a Jihar Bauchi

Mutum uku ne ruwa ya ci a Kogin Kirfi da ke Karamar Hukumar Kirfi, a Jihar Bauchi.

Shugaban Karamar Hukumar Kirfi, Alhaji Abdu Danmalikin Bara ne ya sanar da haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, inda ya ce mutanen sun rasu ne lokacin da ruwa ya yi ambaliya, su kuma suka hau kan gora suna kokarin yin iyo har ruwa ya ci karfinsu suka dulmuya suka rasu.

Alhaji Abdu ya ce duk kokarin da aka yi don ceto su ba a yi nasara ba. Haka kuma ya ce ruwan ya lalata daruruwan gonaki da gidaje, al’amarin da ya jefa mutanen yankin cikin mawuyacin hali.

Ya ce a kokarinta na warware matsalar, Karamar Hukumar Kirfi ta aika a sayo kwale-kwale 10 domin saukaka wa mutane wajen haye kogin, kuma tuni biyu daga cikin kwale-kwalen suka iso.

Ya ce sannan sun bada tallafi ga wadanda bala’in ambaliyar ya rutsa da su, inda ya nanata kudirin gwamnatinsa na kyautata rayuwar jama’a ta hanyar gina hanyoyi da samar da ilimi da samar da isassun kayayyakin kula da lafiya a yankin.

Shugaban ya gode wa Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed saboda goyon bayan da yake ba su don gudanar da ayyukan raya kasa a yankunansu.