Kogin Kaduna ya ci yara biyar
A ranar Talata da ta gabata ne kogin Kaduna ya ci wasu yara biyar da ke sana’ar tuka kwale-kwale a kauyen Rafin Guza da ke Kaduna.Rahotanni daga yankin sun ce yaran sun dace a unguwar a kuma sun dade suna gudanar da sana’arsu ta tuka kwale-kwale suna tsallakar da mutanen kauyen.Aminiya ta je cewa watsuwar […]
????????????????????????????????????

A ranar Talata da ta gabata ne kogin Kaduna ya ci wasu yara biyar da ke sana’ar tuka kwale-kwale a kauyen Rafin Guza da ke Kaduna.
Rahotanni daga yankin sun ce yaran sun dace a unguwar a kuma sun dade suna gudanar da sana’arsu ta tuka kwale-kwale suna tsallakar da mutanen kauyen.
Aminiya ta je cewa watsuwar labari a garin ke da wuya mutanen kauyen suka fito kwai da kwarkwatarsu suka nufi kogin domin ceto rayukan yaran wadanda suka nutse babu ko labarinsu.
Daga bisani rahotanni sun nuna cewa a gano gawarwakin yara uku yayin da biyun kuma ko sama ko kasa.
Shugaban masu binciko yaran Malam Aminu Ibrahim ya ce yaran sun hada da Aliyu Muhammad mai shekara 13 sai Shehu Isma’ila shi ma shekara 13 da Ibrahim Ladan mai shekara 15 sai Mustapha Hamad shi ma shekara 15.
An ce marigayan suna tsallakar da mutane ne daga danbushiya zuwa Rigasa Hayi amma abin da ya faru a ranar sun danganta shi da ikon Allah.
“Wadannan yara kwararru ne a tuka kwale-kwale kuma mun yarda da tukinsu. Sun dauki fasinjoji suka tsallakar da su amma a kan hanyarsu ta dawowa sai kwale-kwalen da suke ciki ya bugi wani abu a cikin ruwan daga nan sai ya kife. Mun gano wasu daga cikin gawarwakin muna kuma ci gaba da neman sauran gawarwakin,” inji Malam Ibrahim.
Shi kuma Mai unguwar Doka a Hayin danbushiya, Alhaji Musa Liman wanda yana cikin masu neman yaran ya danganta abin da ya faru da cewa haka Allah Ya so.
Ya kuma shawarci iyayen yara su tabbatar yaransu sun iya tuka kwale-kwale kafin su rika barinsu suna fiton jama’a.
Alhaji Musa ya koka kan halin rashin kula na ma’aikata agajin gaggawa da na hukumar kashe gobara inda a cewarsa sun ki su kai masu dauki bayan sanar da su abin da ya faru a lokacin.
Tuni aka yi wa mamatan jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.