Kokarin ciro kayar kifi a makogwaro ya sa ta hadiye cokali
Wata mata a kasar China mai suna Lili da ke fama da rashin lafiya, an yi mata tiyata a asibiti bayan ta yi kuskuren hadiye cokalin karfe mai tsawon inci biyar. Matar ta yi hadiye cokalin ne lokacin da take kokarin amfani da shi wajen ciro kayar kifi da ta makale mata a makogoro. Wannan […]
Wata mata a kasar China mai suna Lili da ke fama da rashin lafiya, an yi mata tiyata a asibiti bayan ta yi kuskuren hadiye cokalin karfe mai tsawon inci biyar. Matar ta yi hadiye cokalin ne lokacin da take kokarin amfani da shi wajen ciro kayar kifi da ta makale mata a makogoro.
Wannan marar lafiyan ta kai kwanaki hudu da cokalin da ta hadiye a cikinta ba tare da jin wani ciwo a jikinta ba.
Bayan hoton da aka yi wa mata da na’urar daukar hoton cikin dan Adam (D-ray), likitocin asibitin Shenzhen sun sanya na’urar daukan hoto a cikin hanjin marar lafiyan don gano ciwon da ke damunta.
Matar ta yi kuskuren hadiye cokalin karfen ne kafin bikin al’adu na Kingming da ake yi duk shekara, sai dai a wannan lokaci asibiti na hutun ma’aikata, kamar yadda kafar labarai ta Shenzhen ta ruwaito.
Hakan ya sa Lili ta ki zuwa asibiti na wasu kwanaki saboda ba ta jin wani ciwo a cikinta. Ta ziyarci asibitin Shenzhen Nanshan zuwa wasu kwanaki likitoci suka yi wa mata gwajin ciwon da ke damunta tare da yin hoton cikinta. Sakamakon binciken likitocin ya nuna cewa akwai wani cokalin karfe a cikin hanjin da ta hadiye, hakan ya sa likitoci suka yi kokarin ciro shi daga cikinta.
Likitocin sun samu cokalin a karkace a cikinta har sai da suka saita cokalin a tsaye kafin su fito da shi waje, kamar yadda likitan asibitin Dokta Sun Tingji ya sanar, ya ce sun yi tiyatar a tsawon minti 10.
Dokta Cheng Chunsheng, ya ce matar ta yi kuskuren hadiye cokalin ne lokacin da take kokarin ciro kayar kifi a makogoronta. Cokalin da matar ta hadiye ya kara mata girman ciki da yi mata rauni a hanji.
Rahoton ya kara da cewa, an sallami matar daga asibitin bayan ciro cokalin da ta hadiye.