Koma malanta
Wata rana Jafar da mahaifiyarsa suna hira sai ta ce masa: “Jafar, idan ka gama makaranta wane aiki kake so ka yi?” Sai ya ce: “Ina so in zama malamin makaranta.” Sai mahaifiyar ta ce: “Ai malaman makaranta ba su samun kudi da yawa, ka canza wata sana’ar.” Sai ya ce: “To ina so […]
Wata rana Jafar da mahaifiyarsa suna hira sai ta ce masa: “Jafar, idan ka gama makaranta wane aiki kake so ka yi?” Sai ya ce: “Ina so in zama malamin makaranta.” Sai mahaifiyar ta ce: “Ai malaman makaranta ba su samun kudi da yawa, ka canza wata sana’ar.” Sai ya ce: “To ina so in zama irin masu zama a mota suna cewa: ‘Samaru Samaru, ana ba su kudi” (yana nufin karen mota saboda yana ganin kudi da yawa a hannunsu). Sai mahaifiyar ta ce: “Jafar, Allah Ya raba ka da karen mota koma malantarka.”
Daga Sulaiman Mai Bazazzagiya