Komawa ga Allah ne kadai mafita ga ’yan Najeriya – Malam Bawa

An bayyana cewa hanya guda daya kawai da ‘yan Najeriya za su kama donsamun mafita daga halin rashin tabbas da ake ciki a kasar nan, watokomawa zuwa ga karantarwar da ke cikin saukakkun littafan da Allah yasaukar, tare da bin karantarwarsa sau da kafa. Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ahWa’ikamatissuna na karamar Hukumar […]

Komawa ga Allah ne kadai mafita ga ’yan Najeriya – Malam Bawa

An bayyana cewa hanya guda daya kawai da ‘yan Najeriya za su kama donsamun mafita daga halin rashin tabbas da ake ciki a kasar nan, watokomawa zuwa ga karantarwar da ke cikin saukakkun littafan da Allah yasaukar, tare da bin karantarwarsa sau da kafa.

Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ahWa’ikamatissuna na karamar Hukumar Jama’a Malama Bawa IbrahimKafanchan ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya.

Malamin, ya bayyana cewa ba tare da la’akari da addinin da mutum ke biba, idan kowa da kowa ya kama sahihin karantarwar addininsa zai gacewa dukkaninsu akwai karantarwar tausayi da zaman lafiya da rashinyin bore, tare da yin biyayya ga shugabannin kasa.

Da ya waiwaya kan shugabanni kuwa, Malamin yace dole su tashi tsayekan halin shaye-shaye da matasa suka afka cikinsa a kasar nan,domin hakan ke taimakawa wajen karuwar munanan ayyuka da suka hada dafashi da makami da satar mutane da haddasa rikice-rikice a cikin kasa.

“Misali idan dare yayi za ka ga matasa na ta kwarara zuwa gidajenshaye-shaye da sharholiya, har zuwa tsakar dare ko wayewar gari. Ammaidan ana wani rikici za ka ga gwamnati nan da nan ta kafa dokar hanafita da daddare, saboda masaniyar cewa komai na iya faruwa idan dareyayi don haka gwamnati ta rika sanya ido a kai.” In ji shi.

Da malamin ya juya kan tataburzar da ake ta yi a Jihar Kaduna kan korarwasu malaman makarantun firamare da Gwamnan Jihar Malam NasirEl-Rufa’i yayi, yace kamar yadda gwamnati tayi bayani tana da hujjakan korar wasu daga cikin malaman da tace sun kasa cin jarabawar ‘yan aji hudu sai dai malamin ya yi kira ga gwamnan jihar da cewa idan harbabu wata mafita sai ya salami malaman, to ya zamo duk lokacin da za abasu takardar shaidar cewa an sallame su a hada musu da kudin sallamar bisa ga irin gudummawar da sukayi a baya, inda su kumamalaman da abin ya shafa yayi kira a garesu da su fawwalawa Allah sunrungumi lamarin a matsayin kaddara, sannan su nemi wata sana’a ko waniaikin don Allah ba zai hana su abinda za su ci ba.