Komawa ga Allah ne mafita daga matsalar kasar nan
Shugaban Cocin Deefer Life, da ke kalaba farfesa Andrew Uduigwomen, ya fadi cewa komawa ga Ubangiji t ahanyar addu’a ce mafita daga hal;in da kasar ta samu kanta a ciki, musamman a yankin Arewa maso gabas. Ya fadi haka yayin amsa tambayoyin manema labarai a cibiyar yan jaridu ta kasa da ke Kalaba, jihar Kuros […]
Shugaban Cocin Deefer Life, da ke kalaba farfesa Andrew Uduigwomen, ya fadi cewa komawa ga Ubangiji t ahanyar addu’a ce mafita daga hal;in da kasar ta samu kanta a ciki, musamman a yankin Arewa maso gabas. Ya fadi haka yayin amsa tambayoyin manema labarai a cibiyar yan jaridu ta kasa da ke Kalaba, jihar Kuros Riba.
An tambayi shugaban majami’ar mafita game da matsalar da yankin Arewa maso gabas yake fama da ita.
Addu’a ce kadai mafita halin da Nijeriya ta tsinci kan ta ciki na tabarbarewar al’amura, musamman tsaro da ya sukurkuce a sassa daban-daban na Najeriya zubar da jini da kashe- kashe ya yawaita a kasar nan wanda hakan ya sabawa dokokin madaukakin Sarki Allah
“Wannan hali da yankin ya shiga da kasa baki daya addu’ace mafita, idan addinan na biyu suka dukufa yi wa masu tada kayar baya addu’a Allah ya shirye su, yasa su gane ba a yadda addini da zubar da jini haka kuma kowane addini ba a yada shi a ci nasara da kashe rayuka da babu gaira, babu dalili nasan addinin Musulunci addini ne na zaman lafiya”