Komawar Sadeeq Garo APC alheri ne ga Kano — Dankabo
Dankabo ya ce matashin ɗan siyasar zai taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jihar.
Honarabil Fahad Dankabo, ya taya Sadeeq Aminu Garo murnar komawa jam’iyyar APC, inda ya ce hakan zai taimaka wa ci gaban siyasa a Jihar Kano.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dankabo, ya ce komawar Garo APC, ta nuna jajircewarsa da kuma burinsa na bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.
- Iska ta lalata turaku da wayoyin lantarki a Birnin Kudu, ta jefa dubban jama’a cikin duhu
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a Sakkwato
Ya ce APC jam’iyya ce mai tsari da manufofin samar da nagartaccen shugabanci, bunƙasa tattalin arziƙi da kuma kawo ci gaba mai ɗorewa a Kano da Najeriya baki ɗaya.
Hakazalika, Dankabo, ya yaba da ƙoƙarin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wajen gudanar da harkokin mulki.
Ya ce ya dace a riƙa ƙarfafa duk wani shugabanci da ke fifita walwalar al’umma ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
A cewarsa, dawowar Sadeeq Garo APC alama ce ta haɗin kai da kuma son ci gaban Kano sama da komai.
Dankabo, ya kuma yaba wa Garo bisa irin jagoranci da kulawar da yake nunawa al’umma.

Ya ƙara da cewar matasa irin sa na da muhimmiyar rawa wajen gina makomar jihar.
Ya ƙara da cewa ƙofar APC a buɗe take ga duk masu kishin ƙasa da masu son ci gaban al’umma.
Ya kuma jaddada aniyar jam’iyyar na haɗa kan jama’a domin samar da ingantaccen shugabanci a faɗin Najeriya.
Har ila yau, ya buƙaci Sadeeq Garo da ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ƙarfafa APC da kuma tallafa wa manufofin da za su kawo ci gaba ga Kano da Najeriya baki ɗaya.
“Allah Ya albarkaci Kano, Allah Ya albarkaci Najeriya,” kamar yadda Dankabo ya wallafa.
