Komawar tsohon shugaban Majalisar Katsina APC ya ja hankali
A ranar Litinin da ya gabata ne aka yi bikin karbar tsohon shugaban majalisar dokoki na Jahar Katsina, Hon. Ya’u Umar Gwajo-gwajo daga Jam’iyar PDP zuwa Jam’iyar APC a garin Mai’aduwa. Tsohon Kakakin majalisar wanda ya rike kujerar har sau biyu a jahar a kuma karkashin PDP ya ce, kadan daga cikin dalilansa sun haɗa […]

A ranar Litinin da ya gabata ne aka yi bikin karbar tsohon shugaban majalisar dokoki na Jahar Katsina, Hon. Ya’u Umar Gwajo-gwajo daga Jam’iyar PDP zuwa Jam’iyar APC a garin Mai’aduwa. Tsohon Kakakin majalisar wanda ya rike kujerar har sau biyu a jahar a kuma karkashin PDP ya ce, kadan daga cikin dalilansa sun haɗa da tagwayen nasarorin da aka samu ta fuskar tsaro a matakin kasa da kuma jaha. Kyakkyawan salon shugabanci da kuma lakantar mulkin jaha da Gwamna Masari ke yi, suna daga cikin abubuwan da suka sanya shi canza sheka daga PDP zuwa APC.
Tsohon Kakakin majalisar har ila yau ya kara da cewa a cikin dan karamin lokaci Gwamna Masari ya aiwatar da muhimman ayyuka wadanda suka shafi al’umma kai tsaye wadanda lokaci ba zai bari a zaiyana su ba. “Ina tabbatarwa Gwamna da kuma jam’iyar APC cewa, ni da magoya bayana zamu zamo masu biyayya ga gwamnati da kuma jam’iyya.
Gwamnan Jahar ta Katsina wanda shi ma tsohon Kakakin Majalisar Wakillai ne, Alhaji Aminu Bello Masari ya yi jawabi mai tsawo musamman akan irin nasarorin da gwamnatin Shugaban Qasa, Muhammadu Buhari ta samu tun hawansa bisa karagar mulki, wanda kuma ya ce jama’ar kasar shaida ne. Sannan ya jinjinawa tsohon Kakakin majalisar dokokin na jahar Katsina wanda ya jajirce shi da magoya bayansa a wajen yanke wannan shawara ta canjin sheka na fita daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyar APC mai mulki.
Gwamna Masari har wayau, ya ce, gwamnatin APC za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen ganin an samu zaman lafiya da cigaba musamman a tsakanin matasa da sauran al’umma baki daya ba tare da nuna wani bambanci ba. Gwamnan kazalika, ya ce, ana nan ana shirye-shiryen yin wani jerin gwano da zai gudana a garin Katsina na ‘yan siyasar da suka fice daga jam’ iyunsu suka dawo jam’iyar APC. Shi ma Shugaban Jam’iyar APC na jahar, Alhaji Shitu Masalaha ya yi bayanai akan irin nasarorin da jam’iyar ta samu a siyasance da kuma a gwamnatance. Daga cikin irin jiga-jigan ‘yan siyasar da zasu dawo ko kuma suka dawo a ita jam’iyar ta APC daga PDP kamar yadda Aminiya ta jiyo ana maganarsu sun hada da tsohon Mataimakin Kakakin majalisar dokokin na jahar Katsina wato Komarade Bilya Mohammed Rimi daga shiyyar Katsina da kuma wani tsohon Kwamishina daga shiryar Funtuwa wato, Alhaji Musa Adamu Funtuwa da wasu da dama daga cikin jiga-jigan itar jam’iyyar adawar. Indai za a iya tunawa, daga cikin irin wadanda suka rike wasu mukamai a jahar ta Katsina daga kuma jam’iyar ta PDP, Sanata Ibrahim Ida ne ya fara fita daga PDP zuwa APC, wanda a wancan lokacin ya bayyana dalilansa na barin jam’iyyar da suka hada da mulkin kama karya da rashin mutunta mutun da sauransu.