Kona masallaci: Yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa 10

Mutane 14 suna kwance rai a hannun Allah a asibitin Murtala sakamakon konewar da suka yi

Kona masallaci: Yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa 10

Yawan mutanen da suka rasu ya karu zuwa 10 bayan wani matashi ya banka musu wuta a cikin masallaci suna jam’in Sallar Asuba a Jihar Kano.

Jami’an asibiti sun shaiwa Wakikinmu cewa 14 daga cikin wadanda ake kwantar sakamakon lamarin suna nan rai a hannun Allah.

A mminiya ta kawo rahoto da farko cewa mutum takwas daga cikin wadanda wutar ta koma sun rasu, wasu 20 kuma ana jinyar su a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke garin Kano.

Zuwa ranar Alhamis wakinmu ya koma asibitin inda ya zaga wurin da aka kwantar da 23 daga cikin mutanen.

Jami’an asibitin da suka nemi a boye sunayensu sun tabbatar masa da cewa zuwa lokacin, yawan wadanda suka rasu ya kai mutane tare.

A gefe guda kuma mutum daya da aka kai Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano ya rasu.

A lokacin da ake zagayawa da Wakikinmu dakin da aka kwantar da mutanen a asibitin Murtala, daya daga cikin likitocin ya shaida masa cewa mutane 14 suna kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Aminiya ta ruwaito cewa wani matashi mai shekaru 38 a kauyen Larabar-Abasawa da ke Karamar Hukumar Gazawa ta jihar Kano ya yi wannan aika-aika.

Matashin wanda tuni ya mika kansa ga ’yan sanda, an ruwaito cewa ya yi wannan danyen aiki ne a wani bangare na rikicin gado da ya ki ci ya ki cinyewa a gidansu.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara