An dage shari’ar wanda ya kona mutane a masallaci a Kano
Kotun ta sanya ranar 18 ga watan Yuli, 2024 domin sauraron shaidu a shari’ar mutumin nan da ake zargi ya cinna wa mutane wuta a yayin da suke jam’in sallah Asuba a cikin masallaci a Jihar Kano.
Kotun ta sanya ranar 18 ga watan Yuli, 2024 domin sauraron shaidu a shari’ar mutumin nan da ake zargi ya cinna wa mutane wuta a yayin da suke jam’in sallah Asuba a cikin masallaci a Jihar Kano.
Babbar Kotun Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Zaki ce take sauraron shari’ar koma masallata a garin Larabar Abasawa da ke Karamar Hukumar Gazawa ta jihar
Ana zargin wanda ake kara, Shafi’u Abubakar Gadan, a ranar 15 ga watan Mayu, 2024, ya zuba fetur sanna ya cinna wa mutanen wuta, lamarin da ya janyo da yawa daga cikinsu suka kone da wasu 23 suka mutu.
Bayan karanto masa takardar tuhumarsa, wanda ake zargin ya amsa aikata laifukan na barna da samar da mummunan rauni da kisan ganganci.
Harin Masallacin Kano ya bar marayu 100, mata 13 sun shiga takaba
Masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Salisu Tahir sun shaida wa kotun cewa sun karbi kwafin takardar shigar da karar daga wurin ’yan sanda, amma suna so a sanya sunayen mutanen da suka mutu daga baya a cikin kundin binciken ’yan sanda don ya yi daidai da tuhumar da za su yi masa.
Ya ce, “la’akari da cewa yawan wadanda suka mutu sanadiyyar sanya wutar ya karu, muke rokon kotu ta ba mu wata rana don gabatar da sabon caji don mu sanya adadin yawan mutanen da suka mutu sannan mu gabatar da shaidunmu a gaban kotu.”
Barista Asiya Muhammad Imam daga hukumar da ke bayar da Agajin Shari’a ta Kasa (Legal Aid) ita ce lauyar kariya ga wanda ake tuhuma.
Ta nemi masu gabatar da kara da su sadar da su da sabuwar takardar cajin idan sun sami an shigar da karin sunayen wadanda suka mutun.
Alkalin kotun Mai Shari’a Halhalatul Huza’i Zakariyya ya dage sauraren shariar zuwa ranar 18 da 19 ga watan Yuli don sauraren shaidu.
Sannan ya yi umarni da a ci gaba da tsare wanda ake zargi a gidan gyaran hali. Wa