Konate zai rattaba hannu kan kwantaragin zaman shekaru 4 a Madrid
Wannan ne zai zama kulob na huɗu a rayuwar Konate ta tamaula bayan ya taka leda a FC Sochaux-Montbeliard, RB Leipzig da Liverpool.
Ɗan wasan bayan tawagar ƙasar Faransa, Ibrahima Konate, ya amince da komawa Real Madrid bayan raba gari da Liverpool, kamar yadda wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar ta bayyana.
Ana sa ran Real Madrid za ta sanar da ɗaukar ɗan wasan mai shekara 27 a hukumance ranar Talata, inda zai sanya hannu kan kwantiragin da zai riƙe shi a ƙungiyar har zuwa shekarar 2030.
- MDD ta fara bincike kan zargin tsangwamar Kiristoci a Najeriya
- Isra’ila da Iran na neman a gaggauta tsagaita wuta — Trump
Konate zai haɗu da takwarorinsa na tawagar Faransa a Real Madrid, ciki har da Kylian Mbappe, Aurelien Tchouameni da kuma Eduardo Camavinga.
Wannan ne zai zama kulob na huɗu a rayuwarsa ta tamaula bayan ya taka leda a FC Sochaux-Montbeliard, RB Leipzig da Liverpool.
Tun bayan komawarsa Liverpool shekaru biyar da suka gabata, Konate ya buga wa ƙungiyar wasa 183, inda ya lashe kofin FA da kuma Kofin EFL.
Sai dai ya rasa damar lashe Gasar Zakarun Turai bayan Liverpool ta sha kashi a hannun Real Madrid a wasan ƙarshe na shekarar 2022.
A ƙarƙashin tsohon koci Jurgen Klopp da kuma magajinsa Arne Slot, Konate ya taka muhimmiyar rawa a nasarorin Liverpool, ciki har da lashe gasar Firimiyar Ingila a kakar wasan da ta gabata.
Konate, wanda ya buga wa Faransa wasanni 28, na cikin jerin ’yan wasan da koci Didier Deschamps ya gayyata domin wakiltar ƙasar a Gasar Kofin Duniya da za a soma a makon nan.