Kone masallata: Shafi’u ba shi da tabin hankali —ayansa
An gabatar wa kotun shaidu hudu da suka hada da Dagacin garin Gadan, da yayan wanda ake zargi da kuma kannensa
Babbar Kotun Musulunci da ke Rijiyar Zaki ta fara sauraren shaidu a kan shariar matashin nan Shafiu Abubakar wanda ake zargi da cinna wa masallaci wuta lamarin da ya janyo rasuwar masallata 23.
Aminiya ta rawaito cewa a ranar 15 ga Mayu, 2024 ana tsaka da Sallar Asuba wanda ake zargi, wanda mazaunin garin Gadan ne a Karamar Hukumar Gezawa, ya watsa fetur a cikin masallacin sannan ya cinna wuta, lamarin da ya janyo mutane 23 da ke sallah a suka rasu.
Baya ga wadanda suka rasu, mutum biyu daga ciki sun sami raunika, sannan masallachin da duk kayayyakin cikinsa sun kone kurmus.
Tun a zaman kotun na baya mai gabatar da kara, Barista Salisu Tahir ya shaida mata cewa ana zargin matashin da aikata laifuka hudu da suka hada da kisa da yunkurin aikata kisa da samar da mummunan rauni da barnata dukiya.
Bayan karanto masa takardar karar, wanda ake zargin ya amsa aikata dukkanin laifukan da ake zargin sa da su.
A zaman kotun na yau, mai gabatar da kara ya gabatar wa kotun shaidu hudu da suka hada da Dagacin garin Gadan, da yayan wanda ake zargi da kuma kannensa.
A jawabinsa, shaida na farko wanda kuma shi ne Dagacin garin Gadan, Malam Abdulazeez Yahaya, ya shaida wa kotun cewa kiran sa aka yi aka sanar da shi halin da jama’arsa suka samu kansu a cikiin.
Daga nan suka yi kokarin garzayawa da su Babban Asibitin Sir Sanusi da ke Yankaba kafin daga bisani aka mayar da su Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed.
Da yake bayar da shaida, shaida na biyu wanda kuma yaya ne ga Shafiu. wato Aminu Abubakar, ya bayyana cewa ba wannan ne karo na farko da Shafiu ya fara aikata irin wannan kaba’ira ba.
A cewarsa, a shekarun baya ya farfasa kawunansa, lamarin da ya janyo aka kai shi Asibitin Masu Lalurar Kwakwalwa da ke Dawanau don gwada kwakwalwarsa. inda aka tabbatar da cewa ba shi da wata matsala ta tabin hankali, kamar yadda ake zato.
“Sai dai an ba mu shawara cewa mu nemar masa aikin yi. Anan ne mahaifiyarmu ta sa muka sayar mata da gonarta Naira dubu 350 ta nemi mu yafe wa Shafiu don ya fara sana’a da kudin, inda ya sayo keke mai kafa uku ya ci gaba da harkokinsa.”
A bayanansu daban-daban, kannen wanda ake zargi Shuaibu Ibrahim da Ibrahim Sani sun bayyana cewa suna tsaka da Sallah suka ji tashin wuta a masallaci inda suka yi waje da gudu, wuta tana ci a jikinsu, lamarin da ya jamyo suka sami raunuka a jikinsu.
Sai dai, ita kuma a nata bangaren, lauyar kariya, Barista Asiya Muhammad Imam, ta yi wa ahaidun masu kara tambayoyi.
Mai gabatar da kara, Barista SalisuTahir, ya nemi kotun ta kara ba su wata rana don ci gaba da gabatar da sauran shaidunsu a gaban kotun.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Malam Halhalatul Huzai Zakariyya, ya sanya ranar 24 ga Satumba, 2024, don ci gaba da sauraren shaidu.