kone motocin yakin zaben Jonathan: Jami’an tsaro na ci gaba da kame a Suleja

Jami’an tsaro da suka hada da soji da ’yan sanda na ci gaba da kame a garin Suleja ta Jihar Neja, wanda aka fara a ranar LahadiN da ta gabata bayan wasu matasa sun kone motocin kamfe biyu na Shugaban kasa Goodluck Jonathan da suka biyo ta garin a kan hanyarsu ta zuwa Bidda da […]

kone motocin yakin zaben Jonathan: Jami’an tsaro na ci gaba da kame a Suleja
kone motocin yakin zaben Jonathan: Jami’an tsaro na ci gaba da kame a Suleja

Jami’an tsaro da suka hada da soji da ’yan sanda na ci gaba da kame a garin Suleja ta Jihar Neja, wanda aka fara a ranar LahadiN da ta gabata bayan wasu matasa sun kone motocin kamfe biyu na Shugaban kasa Goodluck Jonathan da suka biyo ta garin a kan hanyarsu ta zuwa Bidda da ke jihar.

Kamen wanda aka ci gaba da yin har zuwa shekaranjiya Laraba lokacin da wakilinmu ya koma garin, wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta a bangare Jam’iyyar PDP, ta ce motocin kaso ne na motocin yakin neman zaben Shugaban kasa Jonathan da aka tura Bidda don yakin neman zabensa a yankin, wanda kuma ya zo daidai da ranar gangamin yakin neman zaben dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP a Jihar Alhaji Umar Gado-Nasko a garin Suleja.
Majiyar ta ce matasan wadanda tun farko aka yi masu alkawarin biyansu Naira dubu bibbiyu a matsayin ladar sanya rigar PDP a wurin taron sun huce hushinsu ne a kan motocin ne sakamakon gaza cika musu alkawari.
Wani limami a kusa da garejin Minna da ke garin Suleja inda sojoji suka kai samame a shekaranjiya, ya ce, sojojin sun kama ’yan uwansa uku a lokacin da suka fito daga gida zuwa masallaci don Sallar Asuba.
Wakilinmu ya samu labarin cewa an kama matasa da dama a unguwannin Magaji da Dawaki da Kwata da kusa da Babbar Kasuwa inda aka wuce da su barikin Zuma.
Da aka tuntubi babban jami’in ’yan sanda na “A” Dibision da ke Suleja, CSP Francis Ekanem ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce bai da hurumin karin haske a kai.