Kongo ta nemi CAF ta canza wurin wasanta da Najeriya saboda cutar Ebola

kasar Kongo ta rubututa wa Hukumar shirya kwallon kafa a Afirka (CAF) wasika na neman a canza wurin wasan da za ta yi da Najeriya a neman hayewa gasar cin kofin Afirka wanda zai gudana a garin Kalaba a ranar 6 ga watan gobe zuwa wata kasa saboda matsalar cutar Ebola.Kongo tana daga cikin kasashen […]

Kongo ta nemi CAF ta canza wurin wasanta da Najeriya saboda cutar Ebola
Kongo ta nemi CAF ta canza wurin wasanta da Najeriya saboda cutar Ebola

kasar Kongo ta rubututa wa Hukumar shirya kwallon kafa a Afirka (CAF) wasika na neman a canza wurin wasan da za ta yi da Najeriya a neman hayewa gasar cin kofin Afirka wanda zai gudana a garin Kalaba a ranar 6 ga watan gobe zuwa wata kasa saboda matsalar cutar Ebola.
Kongo tana daga cikin kasashen Yammacin Afirka da ta kamu da cutar Ebola bayan an samu rahoton mutuwar mutane 12 a Arewacin kasar a ranar Litinin da ta wuce haka kuma Najeriya ma na fama da matsalar cutar tun bayan bullarta.
Sai dai kasar ta Kongo ba ta ambaci inda take so a mayar da wasan ba.
A tattaunawar da kocin Kongo ya yi da manema labarai ya ce “a gaskiya hankalinmu ba zai kwanta ba idan aka ce a Najeriya za mu buga wasan ganin cewa Najeriya da Kongo suna fama da mataslar bullar cutar Ebola don haka zai fi kyau a mayar da wasan wata kasa daban, sai dai matsalar ita ce yadda Kamaru ta rufe kan iyakarta da Najeriya”.
Ita dai Kongo ta samu nasarar shiga gasar ce bayan Hukumar kwallon kafa ta Afirka ta kori kasar Ruwanda bayan an sameta da laifin yin amfani da dan kwallon da bai cancanci ya buga kwallo a wasanta da Kongo ba mai suna Dady Birori.