korafi 367 kadai muka samu a bana – Hukumar PCC

Hukumar amsar korafi da koke-koken jama’a (PCC) a Jihar Jigawa ta ce a cikin shekarar da ta gabata, ta amshi korafe-korafe daga al’umma har guda 367, daga bangarori daban-daban daga fadin jihar. Jawabin hakan ya fito ne daga bakin shugaban hukumar, Alhaji Sa’idu Muhammad Dabi, a wata zantawa da ya yi da manema labarai a […]

korafi 367 kadai muka samu a bana – Hukumar PCC

Hukumar amsar korafi da koke-koken jama’a (PCC) a Jihar Jigawa ta ce a cikin shekarar da ta gabata, ta amshi korafe-korafe daga al’umma har guda 367, daga bangarori daban-daban daga fadin jihar.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin shugaban hukumar, Alhaji Sa’idu Muhammad Dabi, a wata zantawa da ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya ce daga cikin korafe-korafen guda 367 da jama’a suka gabatar a gaban hukumar ta su, sun sami ikon warware korafe-korafe guda 257 kuma yanzu sauran guda 110 suka rage da ba a warware ba. Ya ce za su iya fadawa cikin shekara mai zuwa kafin a sami ikon kammala su.

Ya shawarci jama’a, musamman wadanda ba su san da zaman hukumar ba da kuma wadanda suka san da ita, su rika gabatar da korafe-korafensu a gabanta, domin neman hakkinsu da ya makale a wajen aiki ko kuma a gaban alkali, ko kuma a wajen abokan hulda da suke neman zalintarsu.

Ya bayyana cewa hukumar tana da lauyoyi da take amfani da su wajen kwato wa talakawa hakkinsu da ya makale a wajen duk wanda yake neman ya cuce su. Ya ce aikinsu bai tsaya iya nan ba, koda wasika ce ka aika ta makale ko sako ta hanyar gidan waya, in bai je ba, ya makale ko aka samu matsala, hukumar tana bin diddigi wajan ganin ta bi duk hanyar da ta kamata, domin kwato wa mutum hakkinsa.

Dabi ya yaba wa Hukumar Kula Da ’Yan Fansho ta Jihar Jigawa saboda irin hadin kan da take ba ma’aikatansa a lokacin da suka je gabanta da wata bukata ta neman taimako a kan wani ko wata da take da matsala a kan hakkinta na kudin fansho. Ana warware matsalarsu cikin ruwan sanyi ba tare da an sami wata matsala ba.

Kwamishinan hukumar ya ci gaba da cewa amma hukumar tasa na fuskantar matsala tsakaninta da hukumar kasa da safiyo ta Jihar Jigawa, domin a duk lokacin da wata matsala ta gona ko fili ko gida ta faru, wadda hukumar za ta iya taka rawa amma sau da yawa sai a wayi gari karamar matsalar da za a iya warware ta cikin karamin lokaci sai ta dauki dogon lokaci ba a warware ta ba.

Ya kuma ja kunnen jama’a da su guji gabatar da korafi a gabansu idan har korafin yana gaban shari’a, domin ita hukumar ba ta daukar mataki a kan korafin da yake gaban kotu ko kuma tsakanin mutun da mutum; sai dai tsakanin mutun da hukuma, shi ne ta fi taka muhimmiyar rawa domin ta taimaka wa mutun ya samu hakkinsa.