Korar Ministoci: Jonathan ya fara nuna jan ido akan 2015

Na fahimta kamar yadda shi shugaban kasa ya yi mana bayani, ya fahimci irin yadda gwamnatinsa take tafiya, ya kuma sanya wa kansa wasu kudurorin da yake so ya cimmawa nan da shekaru biyu masu zuwa, don haka abin da yake shi ne ya iya daidaita Majalisar Zartaswar , ta yadda zai iya cimma kudurorinsa […]

Korar Ministoci: Jonathan ya fara nuna jan ido akan 2015
Korar Ministoci: Jonathan ya fara nuna jan ido akan 2015

Na fahimta kamar yadda shi shugaban kasa ya yi mana bayani, ya fahimci irin yadda gwamnatinsa take tafiya, ya kuma sanya wa kansa wasu kudurorin da yake so ya cimmawa nan da shekaru biyu masu zuwa, don haka abin da yake shi ne ya iya daidaita Majalisar Zartaswar , ta yadda zai iya cimma kudurorinsa na aniyar kawo sauyi cikin tafiyar da mulkin kasar nan. Kar ka dada, kar ka raga, wannan shi ne dalilan da suka sa ya bullo da wadannan sauye-sauye, a wannan lokaci .’’
Wani daga cikin yankin jawabin Ministan yada labarai Mista Labaran Maku ke nan ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron mako-mako na Majalisar zartaswa ta kasa a fadar gwamnati tarayya a ranar Larabar makon jiya, inda Ministan ya bada shelar cewa shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya sauke wasu Ministoci tara daga  kan mukamansu nan take, saukewar da Ministan ya yi ta jaddada ko kadan ba ta da alaka da siyasa. Ministocin da aka sauke sun hada da shidda manyan Ministoci  da kuma uku Ministocin kasa.
Ministoci manya sun hada da Olugbenga Ashiru na Harkokin kasashen waje da Farfesa Rukayyatu Rufa`i ta ma`aikatar ilmi da Dokta Shamsuddeen Usman na Tsare-tsaren kasa da Hajiya Hadizah Mailafiya ta Ma`aikatar kare muhalli da Uwargida Amal Pepple ta ma`aikatar filaye, gidaje da raya birane da Mista Ekan Bassey Ewa, na ma`aikatar Kimiya da Fasaha. Ministocin kasa ukun da fyadin `yan kadayyar shugaba Jonathan ya shafa su ne, Uwargida Erele Obada ta ma`aikatar tsaro da Uwargida Zainab Kuchi ta ma`aikatar makamashi da Alhaji Bukar Tijani na ma`aikatar ayyukan gona.
Kodayake Minista Labaran Maku da duk wani na kusa da shugaba Jonathan, kai har ma da wasu da ake ganin don su aka kori Ministocin kamar Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido suna ta musanta zargin cewa da wata nufaka aka kori Ministocin, amma dai `yan kasa da dama, musamman masu bin diddikin harkokin siyasar kasar nan, suna da ja akan lalle kam da walakin wai goro a cikin miya. Masu irin wannan ra`ayi suna ganin shugaban kasa ya yi haka ne don ya fara nuna wa wadancan gwamnoni bakwai da suka balle, suka kuma kafa sabuwar jam`iyyar PDP, shi fa ba kanwar lasa ba ne, kuma ba gudu ba ja da baya daga wurinsa akan sai ya nemi takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2015, in Allah Ya kaimu.
Alal misali kowa ya san an sauke Farfesa Rukayyatu ce don Gwamna Alhaji Sule Lamido na jiharta ta Jigawa, wanda kusan ma shi ke jagoran wadancan gwamnoni bakwai da suke rigima da shugabancin PDP ta Alhaji Bamanga Tukur. Haka labarin yake wajen sauke Hajiya Zainab Kuchi, da take `yar asalin Jihar Neja, inda gwamnanta Dokta Ma`azu Babangida Aliyu yake tsakiyar waccan adawa, akwai kuma uwargida Erelu Obada ta ma`aikatar Tsoro da ake jin dangantakarta da Sakataren sabuwar PDP, wanda a da shike tsohon gwamnan jihar Osun kuma tsohon Sakataren jam`iyyar PDP tsagin Alhaji Bamanga Tukur, waccan danganta ce ta sa aka yi waje da ita.
    Sauran Ministocin da ake zargin waccan rigima ta bangarorin jam`iyyar PDP biyu ta ci su, sun hada da Olugbenga Ashiru tsohon Ministan Harkokin kasashen waje da aka ce na hannun daman tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ne. Akwai kuma Uwargida Amal Pepple da take `yar asalin Jihar Ribas ce, inda rigima tafi kamari tsakanin Shugaba Jonathan da Gwaman Jihar Cif Rotimi Ameachi, wanda yake shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan.
Kamar yadda na fadi a wannan shafi a makalata ta rana wata yau, mai taken “Jam`iyyar PDP karamar magana ta zama babba,” na yi hasashen cewa idan dai ba wani ikon Allah ba, yana da wuya a samu shiryawa tsakanin shugaban kasa da gwamnoninnan bakwai, duk da kokarin hakan da ake. Bayan sallamar wadancan Ministoci sai kuma ga shi an yi taro tsakanin shugaban kasa da wadancan gwamnoni bakwai a ranar Lahadin da ta gabata. A sanarwar bayan taro da Gwamnan Jihar Neja ya karanta wa manema labarai ya fadi cewa suna kokarin sasanta junansu, a bisa ga haka ne ma aka nemi kowane bangare da ya mayar da takobinsa, a kuma daina kalaman batanci ga juna, an kuma tsaida ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa in Allah Ya kaimu don ci gaba da wannan tattaunawa.
  Mai yiwuwa abin da ya sa aka yi waccan hadu da shugaban kasa da wadancan gwamnoni, bata rasa nasaba da irin kalaman da aka ce wai shugaban wancan sulhi wato Cif Obasanjo ya fadawa shugaba Jonathan cewa muddin yana so a shirya, to sai ya manta da batun tsayawa takarar 2015, sannan kuma Alhaji Bamanga Tukur ya sauka daga kan shugabancin jam`iyyar PDP. Wadannan bukatu biyu ko kusa shugaba Jonathan da Alhaji Bamanga Tukur ba sa son jin su, bare su amince da su.
Ba don kome ba suke da wahalar karbuwa daga shugaba Jonathan, sai dai irin zugar da ake ta masa musamman daga mutanen yankinsa na Neja Delta irin su Cif Tony Anenih shugaban Kwamitin Amintattun jam`iyyarsu ta PDP na kasa baki daya da sauran wasu masu son a ci gaba da yi da su a cikin tafiyar ta shugaba Jonathan da kuma irin yadda shugaba Jonathan yake tunanin ba zabe ake ba a kasar nan don haka gare shi da sauran masu tunani irinsa samun tikitin tsayawa takara a jam`iyyar PDP, shi ke babban lasisin cin zabe a kasar nan, don haka koda goyan bayan wadancan gwamnonin jihohi ko babu, in dai ya samu takara ya ci zabe. Shi kuwa tsoho Alhaji Bamanga Tukur, da ya yi ta nanata ba inda zaya, yana nan zama daram dam, babban burinsa bai wuce ya ga babban dansa ya zama gwamnan jiharsa ta Adamawa ba.
  Don haka sauke wadancan Ministoci da ya yi tabbas ta kara tabbatar wa duk wanda yake shakka cewa ga shugaba Jonathan, ba gudu ba ja da baya akan sai ya tsaya waccan takara, don haka ni banga laifinsa ba da ya fara nuna wa gwamnoni da duk wani mai son ya ja da mulkinsa, cewa ba su isa ba. Addu`armu dai ba ta wuce  Allah Ka ceci kasar nan, amma shugabanninta na da da na yanzu ba abin da ke gabansu sai irin yadda za su ci gaba da rike kambin yadda za su ci gaba da mallakarmu ta ko wane hali.