Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami
Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami a tekun da aka fi sani da tekun Japan. Kamfanin Dillancin Labarai na Yonhap ya ce, rundunar sojin Koriya ta Kudu ta ce Koriya ta Arewa ta gwada harba makami mai linzami a tekun Japan. Sanarwar da aka fitar ba ta bayyana samfurin makamin da kuma […]
Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami a tekun da aka fi sani da tekun Japan. Kamfanin Dillancin Labarai na Yonhap ya ce, rundunar sojin Koriya ta Kudu ta ce Koriya ta Arewa ta gwada harba makami mai linzami a tekun Japan.
Sanarwar da aka fitar ba ta bayyana samfurin makamin da kuma tafiyar da ya yi kafin ya fada a teku ba; amma ana ci gaba da bincike da sanya ido a yankin.
A ranar 28 ga Nuwamban bara ne Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami a karo na karshe. Tsawon shekara guda ke nan Amurka da Koriya ta Arewa suke tattaunawa kan a daina samar da makaman nukiliya: amma a watan Oktoban bara aka katse tattaunawar da ake yi a kasar Sweden.
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un ya saka wasu sharudda ga Amurka matukar tana so su ci gaba da tattaunawar; kuma idan ba haka ba daga karshen watan Janairun bana za su dawo da gwajin makamai masu linzami da ke cin dogon zango kuma ake iya sarrafa su daga nesa.