Koriya ta Kudu za ta gina tashar wutar lantarki daga hasken rana ta $12.5m a Najeriya

Kasar ta ce ta kirkiro aikin ne don magance matsalar lantarki, musamman a karkara.

Koriya ta Kudu za ta gina tashar wutar lantarki daga hasken rana ta $12.5m a Najeriya

Tutocin Koriya ta Kudu da Najeriya

Gwamnatin kasar Koriya ta Kudu a ranar Litinin ta ce  za ta gina tashoshin wutar lantarki mai amfani da hasken rana wadda za su kai na Dalar Amurka miliyan 12.4 a Najeriya.

Mataimakin Shugaban Cibiyar Bunkasa Fasaha ta Jamhuriyar Koriya, Kim Jeong-Wook, ne ya bayyana hakan a Abuja.

A cewarsa, an kirkiro aikin ne don magance matsalar wutar lantarki, musamman a yankunan karkara.

Ya ce aikin zai kara yaukaka dankon dangantaka tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Koriyar.

Mista Kim ya kuma ce aikin zai bunkasa tattalin arziki, ya samar da ayyukan yi, ya magance talauci sannan ya bunkasa rayuwar mazauna yankunan da aikin zai shafa.

“Bugu da kari, ta hanyar magance kalubalen makamashi tsakanin birane da yankunan karkara, aiki kuma zai magance kalubalen rashin ci gaba a kasa,” inji shi.