Koro ’Yan Najeriya: Za mu sa kafar wando da Ghana —Lai Mohammed

Najeriya za ta dauki mataki kan matsin lambar da ake wa ‘yan kasarta a Ghana

Koro ’Yan Najeriya: Za mu sa kafar wando da Ghana —Lai Mohammed

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed

Gwamnati Tarayya ta kalubalanci kasar Ghana kan da koro ‘yan Najeriya mazauna can da take yi, ta ce ba za ta kara amincewa da cin mutunci ba.

Najeriya ta kuma nuna damuwa kan hare-hare da cin zarafin da hukumomi ke yi wa ’yan Najeriya a Ghana, wadda ta koro ’yan Najeriya 825 cikin shekara daya.

Ghana ta kulle shagunan ’yan Najeriya da dama a birnin Accra bisa zargin kin biyan harajin Dala miliyan daya.

Ma’aikatar Kasuwancin Ghana ta ba masu shaguna mako biyu su biya kudaden ko kuma su kulle shagunan.

Ministan Watsa Labaran Najeriya, Mohammed ya fitar, ya yi tir da irin rahotannin da kafafen labarai a Ghana ke fitarwa, wadanda ya ce na iya kawo kyamar ‘yan kasuwar Najeriya a Ghana.

Lai Mohammed ya yi kira ga ’yan Najeriya mazauna Ghana da su zamo masu bin doka, kar su dauki doka a hannunsu duk da tsangwamar da suke fuskanta a can.

Ya ce gwamnati na nan tana dubar hanyoyin da za ta bin domin a sama musu saukin halin da suke ciki.

Ministan ya kuma lissafa abubuwa da dama na cin zarafi da aka yi wa Najeriya da suka hada da kwace Ofishin Jakadanci Najeriya mai kimanin shekara 50, duk da hakan ya saba wa yarjejeniyar Bienna.

Ya kuma koka rushe ginin Ofishin Jakadancin Najeriya a birnin Accra, tare da koro ’yan Najeriya daga kasar.

“Gwamnatin Tarayya na tattara wadannan bayanan cin mutunci da hukumomin Ghana ke wa Najeriya da ’yan Najeriya a kasarta”.

Lai Mohammed ya kuma ce duk da cewar akwai ’yan Ghana fiye da miliyan daya a Najeriya, ba a taba nuna musu kiyayya irin wadda ake yi wa ’yan Najeriya a Ghana ba.