Kotu a Kano ta aike da barawon kare gidan gyaran hali
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan matashin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa.
Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Fagge a Jihar Kano ta aike da wani matashi zuwa gidan gyaran hali bayan ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa na satar kare.
Matashin, mai suna Alhassan Yusuf, mai kimanin shekara 21, dai ya amsa aikata laifin satar karen wanda darajarsa ta kai kusan Naira 10,000.
- Dakarun Saudiyya sun kashe mayakan juyin juya halin Iran a Yemen
- Babu rigar mama ta zinare a kayan da aka kwace daga Diezani —Shugaban EFCC
Alhassan dai mazaunin unguwar Tudun Maliki ne da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.
Ana tuhumarsa ne da laifuffuka guda biyu da suka jibanci ketare iyaka da kuma sata.
Tuni dai ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawar.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Bello Khalid, ya umarci a tsare wanda ake tuhumar a gidan gyaran hali, sannan ya dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar uku ga watan Disamban 2021 domin yanke hukunci.