Kotu a Kano ta yanke wa barawon intanet daurin shekara 1

Kotun ta ci shi tarar kudi Naira miliyan daya.

Kotu a Kano ta yanke wa barawon intanet daurin shekara 1

Jami’an EFCC a bakin aiki

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ta yanke wa wani mai damfara ta intanet daurin shekara daya a gidan yari da tarar Naira miliyan daya.

Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ce ta cafke matashin tare da gurfanar da shi a gaban kotun da ke karkashin jagorancin mai shari’a A. M. Liman.

Bincike ya gano cewa matashin ya kware wajen satar kudade da damfara ta intanet tare da sanya wasu cikin harkar.

Bayan cafke shi, an samu mota kirar Mercedes Benz GLK, kwamfuta guda biyu, na’urar fitar da takarda da kuma waya kirar iPhone 12 a wurinsa.

Bayan gabatar da shi a gaban kotun, matashin ya amsa laifin da ake tuhumar shi da aikatawa tare da neman afuwar kotun.

Alkalin kotun Liman ya yanke masa hukuncin daurin shekara daya tare da tarar kudi Naira miliyan daya.

Kotun ta kuma bayar da umarnin kwace dukkanin kayan da aka samu a wajensa tare da mika su ga Gwamnatin Tarayya.