Kotu na neman Grace Mugabe a Afirka ta Kudu

Hukumoni a Afirka ta Kudu na neman matar tsohon Shugaban Zimbabwe Misi Grace Mugabe don ta gurfana a gaban wata kotu domin amsa tuhumar da ake yi mata na cin zarafin wata matashiya mai tallata kayan kawa. Mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Afirka ta Kudu Bishnu Naidoo, ya tabbatar da ba da takardar […]

Kotu na neman Grace Mugabe a Afirka ta Kudu

Hukumoni a Afirka ta Kudu na neman matar tsohon Shugaban Zimbabwe Misi Grace Mugabe don ta gurfana a gaban wata kotu domin amsa tuhumar da ake yi mata na cin zarafin wata matashiya mai tallata kayan kawa.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Afirka ta Kudu Bishnu Naidoo, ya tabbatar da ba da takardar sammaci ga uwargidan tsohon shugaban Zimbabwe Grace Mugabe a kan zargin cin zarafin wata matashiya.

Mista Naidoo ya bayyana cewa an bayar da takardar ce tun Alhamis din da ta gabata.

BBC ya ruwaito daga Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa Mista Naidoo ya ce ’yan sandan kasar na neman taimako daga ’yan sandan duniya (Interpol) domin ganin takardar sammacin ta isa gare ta.

Wannan yunkurin na bayar da takardar sammaci na zuwa ne bayan da a watan Yuli wata kotu a kasar ta soke kariyar diflomasiyya da Uwargidan Mugaben ke da ita.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta jawo cece-ku-ce bayan da ta kyale Grace Mugabe ta fice daga kasar bayan zarginta da cin zarafin matashiyar a wani otel da ke Johannesburg.

Har yanzu, babu tabbacin ko Afirka ta Kudu za ta hukunta matar Mugaben.

Laifin da ake zarginta da shi ya auku ne wata uku kafin saukar Robert Mugabe daga kan mulkin Zimbabwe.

Jami’ar Bayero ta Kano ta kori ɗalibai 78

Kotu ta yi watsi da ayyana kungiyar Palasdinawa a matsayin ’yar ta’adda

Wata matar aure ta sari mijinta da adda 

Lakurawa sun kashe fararen hula 20 a Kebbi