Kotu sa a kashe dan fashi ta hanyar yatayewa
An kama matashi mai shekara 24 da laifin fyade da kuma fashi da makami.
Kotu ta yanke wa wani matashi mai shekara 24 hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Mai Shari’a Oluwatoyin Abodunde, ta yanke masa hukuncin ne a ranar Talata bayan kama shi da laifin aikata fashi da kuma fyade da ake tuhumar sa da aikatawa.
- Kifi ya hadiye dan ninkaya ya amayar da shi da rai
- Za a rataye ’yan bindiga da masu satar mutane a Neja
Kotun da ke zamanta a garin Ado Ekiti, hedikwatar Jihar Ekiti, ta ce laifuka uku da ake tuhumar sa da aikawata sun tabbata, “An kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya; Allah Ya jikan sa.”
Laifukan da kotun ta kama shi da aikatawa na da alaka da fashi da makami da kuma fyade a ranar 30 ga watan Oktoba 2015, a layin Oda Ponna, da ke unguwar Omuo Ekiti.
Baya ga ayyukan fashi, matsalar fyade ta kazanta a sassan Najeriya, wanda ya kai ga kira-kirayen yanke hukunci mai tsauri ga masu aikatawa domin zama izina ga masu mummunar dabi’ar.
A kan haka ne wasu jihohi suka kafa dokar yanke hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai ko dandaka ga masu aikata fyade.