Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe

An samu Farfesan da laifin sauya sakamakon zaɓe da kuma yin rantsuwar ƙarya a kotu.

Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe

Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa Farfesa Ignatius Uduk hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari kan laifin sauya sakamakon zaɓe.

An gurfanar da Farfesan kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da gazawa wajen aiwatar da aikinsa, sauya sakamakon zaɓe, da kuma yin rantsuwar ƙarya a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe.

Lamarin ya shafi zaɓen ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a Essien Udim a shekarar 2019.

A ranar Laraba ne, Mai shari’a Bassey Nkanang ya same shi da laifin sauya sakamakon zaɓe da yin rantsuwa bisa ƙarya.

Hakan ya sa alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan yari kan kowane laifi.

Farfesa Uduk, wanda shi ne jami’in tattara sakamakon zaɓe a lokacin, an fara gurfanar da shi a gaban kotu tun ranar 9 ga watan Disamban 2020.

Hakazalika, ya kasance malami a fannin Human Kinetics a Jami’ar Uyo.

Baffa Bichi da Barau Jibrin sun gana a Abuja

MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP

Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas

Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo