Kotu ta ɗaure matashi shekara 2 kan satar wayoyi a Kano
Matashin ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su.
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula.
An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji.
- ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano
- ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna
A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin.
An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin jama’a.
Matashin ya amsa laifukan nan gaba ɗaya.
Alƙalin kotun, Khadi Umar Lawan Abubakar, ya yanke masa hukuncin watanni shida a gidan yari ko kuma ya biya tarar Naira 20,000 kan laifin haɗa baki.
Ɗaurin shekara ɗaya a gidan yari kan satar waya, da kuma wata shekara ɗaya kan tayar wa jama’a hankali, ba tare da zaɓin biyan tara ba.