Kotu ta ɗaure matashi wata 6 saboda satar wake a Ibadan

Matashin zai yi zaman wakafi na watanni shida saboda satar wake.

Kotu ta ɗaure matashi wata 6 saboda satar wake a Ibadan

Kotu

Wata Kotun Al’adu da ke birnin Ibadan na Jihar Oyo, ta yanke wa wani matashi hukuncin cin sarka ta watanni 6 a Gidan Dan Kande.

Kotun a ranar Juma’a ta yanke wa matashin mai suna Samuel John hukuncin ne bayan samunsa da laifin satar ɗanyen wake da darajarsa ta kai kimanin Naira dubu 20.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Sukurat Yusuf ta yanke wa matashin dan shekara 20 wannan hukunci ne bayan shi da kansa ya amince da aikata laifuka biyu na fasa gida da sata da aka tuhume shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa kotun ta yanke wa matashin hukumcin ne ba tare da bayar da zabin biyan tarar kudi a madadin daurin ba.

Mai Shari’a Sukurat ta bayar da umarnin a tisa keyar matashin zuwa gidan gyaran hali na Agodi da ke Ibadan, inda zai yi zaman kaso na wa’adin wata 6 da kotun ta yanke masa.

Tun da farko sai da mai gabatar da kara, Mista Philip Amusan ya shaida wa kotun cewa Samuel John ya aikata laifin ne da misalin karfe 6 na yamma a ranar 2 ga watan Satumba da muke ciki, a kauyen Omi-Adio a kusa da Ibadan.

Ya ce a daidai wannan lokaci ne ya fasa gidan wata mata mai suna Felicia Oni, inda ya sace wannan kayan abinci mai darajar kudi Naira dubu 20.

Ya ce laifin da ya aikata ya saba wa kundin Dokokin Jihar Oyo na shekarar 2000 sashe na 411 da 390(9).

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara